Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Saboda haka ya ba da su ga aiki mai wuya; suka yi tuntuɓe, kuma ba mai taimako.

  2. Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuwa cece su daga damuwarsu.

  3. Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane,

  4. gama ya farfashe ƙofofin tagulla ya kuma ragargaza ƙyamaren ƙarfe.

  5. Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuwa cece su daga damuwarsu.

  6. Ya ba da umarninsa ya kuma warkar da su ya kuɓutar da su daga kabari.

  7. Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane.

  8. Bari su miƙa hadaya ta godiya su kuma ba da labarin ayyukansa da waƙoƙin farin ciki.

  9. Sun ga ayyukan Ubangiji, ayyukansa masu banmamaki a cikin zurfin teku.

  10. Gama ya yi magana ya kuma sa iska mai ƙarfi ta tashi ya ɗaga raƙuman ruwa sama.

  11. Sai suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuwa fitar da su daga damuwarsu.

  12. Suka yi murna sa’ad da wuri ya kwanta, ya kuma bishe su zuwa inda suka so su kai.

  13. Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane.

  14. Bari su ɗaukaka shi cikin taron mutane su kuma yabe shi cikin taron dattawa.

  15. a can ya kai mayunwata su yi zama, ya kuma samo birnin da za su zauna.

  16. Amma ya fid da mabukata daga wahalarsu ya kuma ƙara iyalansu da tumakinsu.

  17. Duk mai hikima, bari yă ji waɗannan abubuwa yă kuma lura da ƙauna mai girma ta Ubangiji.

  18. Waƙa ce. Zabura ta Dawuda. Zuciyata tsayayyiya ce, ya Allah; zan rera in kuma yi kiɗi da dukan raina.

  19. Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai; zan rera game da kai cikin mutane.

  20. Gama ƙaunarka da girma take, bisa fiye da sammai; amincinka ya kai sarari.

  21. A ɗaukaka ka, ya Allah, a bisa sammai, bari kuma ɗaukakarka ta kasance a bisa dukan duniya.

  22. Ka cece mu ka kuma taimake mu da hannunka na dama, domin waɗanda kake ƙauna su kuɓuta.

  23. Allah ya yi magana daga wurinsa mai tsarki, “Ciki nasara zan raba Shekem in kuma auna Kwarin Sukkot.

  24. Mowab shi ne kwanon wankina, a kan Edom zan jefa takalmina; a bisa Filistiya zan yi kirari cikin nasara.”

  25. Ba kai ba ne, ya Allah, kai da ka ƙi mu ba ka kuwa fita tare da mayaƙanmu?