God
Ayoyin da suka ambaci God
Tare da Allah za mu yi nasara, zai kuma tattaka abokan gābanmu.
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce. Ya Allah, wanda nake yabo, kada ka yi shiru,
Ka naɗa mugun mutum yă yi hamayya da shi; bari mai zargi yă tsaya a hannun damansa.
Bari a tuna da laifin kakanninsa a gaban Ubangiji; bari kada a taɓa shafe zunubin mahaifiyarsa.
Bari zunubansu su kasance a gaban Ubangiji kullum, don yă sa a manta da su daga duniya.
Bari wannan yă zama sakayyar Ubangiji ga masu zargina, ga waɗanda suke mugayen maganganu a kaina.
Amma kai, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ka yi da ni da kyau saboda sunanka; ta alherin ƙaunarka, ka cece ni.
Ka taimake ni, ya Ubangiji Allahna; ka cece ni bisa ga ƙaunarka.
Bari su san cewa hannunka ne, cewa kai ne, ya Ubangiji, ka yi shi.
Za su iya la’anta, amma kai za ka sa albarka; sa’ad da suka tasar za su sha kunya, amma bawanka zai yi farin ciki.
Da bakina zan ɗaukaka Ubangiji sosai; cikin babban taro zan yabe shi.
Gama yana tsaya a hannun damar mai bukata, don yă cece ransa daga waɗanda suke hukunta shi.
Ta Dawuda. Zabura ce. Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana, sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.”
Ubangiji zai fadada ikon sandan mulkinka daga Sihiyona za ka yi mulki a tsakiyar abokan gābanka.
Rundunarka za su so yin yaƙi a ranarka ta yaƙi. Saye cikin ɗaukaka mai tsarki, daga cikin ciki na safiya za ka karɓi raɓar ƙuruciyarka.
Ubangiji ya rantse ba zai kuma canja zuciyarsa ba, “Kai firist ne har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.”
Ubangiji yana a hannun damanka; zai murƙushe sarakuna a ranar fushinsa.
Yabi Ubangiji. Zan ɗaukaka Ubangiji da dukan zuciyata a cikin majalisar masu aikata gaskiya da kuma a cikin taro.
Ayyukan Ubangiji da girma suke; dukan waɗanda suke farin ciki da su suna tunaninsu.
Ayyukansa masu ɗaukaka da kuma daraja ne, adalcinsa kuma zai dawwama har abada.
Ya sa a tuna da abubuwa masu banmamaki nasa; Ubangiji mai alheri ne mai tausayi kuma.
Yana ba da abinci ga waɗanda suke tsoronsa; yakan tuna da alkawarinsa har abada.
Ya nuna wa mutanensa ikon ayyukansa, yana ba su ƙasashen waɗansu al’ummai.
Ayyukan hannuwansa masu aminci ne da kuma gaskiya; dukan farillansa abin dogara ne.
Yana ba da ceto ga mutanensa; ya kafa alkawarinsa har abada, tsarki da banrazana ne sunansa.