Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. mu ne masu ɗaukaka Ubangiji, yanzu da har abada kuma. Yabi Ubangiji.

  2. Ina ƙaunar Ubangiji, gama ya ji muryata; ya ji kukata ta neman jinƙai.

  3. Domin ya juye kunnensa gare ni, zan kira gare shi muddin ina da rai.

  4. Sai na kira ga sunan Ubangiji na ce, “Ya Ubangiji, ka cece ni!”

  5. Ubangiji mai alheri ne da kuma mai adalci; Allahnmu yana cike da tausayi.

  6. Ubangiji yana tsare masu tawali’u; sa’ad da nake cikin tsananin bukata, ya cece ni.

  7. Ka kwantar da hankali, ya raina, gama Ubangiji mai alheri ne a gare ka.

  8. Gama kai, ya Ubangiji, ka ceci raina daga mutuwa, idanuna daga hawaye, ƙafafuna daga tuntuɓe,

  9. don in iya tafiya a gaban Ubangiji a ƙasar masu rai.

  10. Yaya zan sāka wa Ubangiji saboda dukan alherinsa gare ni?

  11. Zan daga kwaf na ceto in kuma kira ga sunan Ubangiji.

  12. Zan cika alkawurana ga Ubangiji a gaban dukan mutanensa.

  13. Abu mai daraja a gaban Ubangiji shi ne mutuwar tsarkakansa.

  14. Ya Ubangiji, da gaske ni bawanka ne; ni bawanka ne, ɗan baiwarka; ka ’yantar da ni daga sarƙoƙi.

  15. Zan yi hadayar godiya gare ka in kuma kira bisa sunan Ubangiji.

  16. Zan cika alkawurana ga Ubangiji a gaban dukan mutanensa,

  17. a filayen gidan Ubangiji, a tsakiyarki, ya Urushalima. Yabi Ubangiji.

  18. Yabi Ubangiji, dukanku al’umma; ku ɗaukaka shi, dukanku mutane.

  19. Gama ƙaunarsa da girma take gare mu, amincin Ubangiji kuma madawwami ne har abada. Yabi Ubangiji.

  20. Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.

  21. Bari Isra’ila yă ce, “Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”

  22. Bari gidan Haruna yă ce, “Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”

  23. Bari waɗanda suke tsoron Ubangiji su ce, “Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”

  24. Cikin azabata na yi kuka ga Ubangiji, ya kuwa amsa ta wurin ’yantar da ni.

  25. Ubangiji yana tare da ni; ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai yi mini?