Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Dawuda ya ce, “Ɗana Solomon matashi ne kuma bai gogu ba, kuma gidan da za a gina wa Ubangiji zai zama mai ƙayatarwa ƙwarai, sananne da kuma mai daraja a idon dukan al’ummai. Saboda haka zan yi shirye-shirye saboda shi.” Sai Dawuda ya yi ɗumbun shirye-shirye kafin mutuwarsa.

  2. Sa’an nan ya kira ɗansa Solomon ya umarce shi yă gina gida domin Ubangiji, Allah na Isra’ila.

  3. Dawuda ya ce wa Solomon, “Ɗana, na yi niyya a zuciyata in gina gida saboda Sunan Ubangiji Allahna.

  4. Amma wannan maganar Ubangiji ta zo mini, ‘Ka zub da jini mai yawa ka kuma yi yaƙe-yaƙe masu yawa. Ba za ka gina gida domin Sunana ba, domin ka zub da jini da yawa a duniya a idona.

  5. Amma za ka haifi ɗa wanda zai zama mutumin salama da kuma hutu, zan kuma ba shi hutu daga dukan abokan gābansa a kowane gefe. Za a kira shi Solomon, zai kuma kawo wa Isra’ila salama da natsuwa a zamanin mulkinsa.

  6. Shi ne wanda zai gina gida saboda Sunana. Zai zama ɗana, ni kuma zan zama mahaifinsa. Zan kafa kujerar sarautarsa a bisa Isra’ila har abada.’

  7. “Yanzu, ɗana, Ubangiji ya kasance tare da kai, bari kuma ka yi nasara ka kuma gina gidan Ubangiji Allahnka, kamar yadda ya ce za ka yi.

  8. Bari Ubangiji ya ba ka basira da fahimi sa’ad da ya sa ka shugaba a bisa Isra’ila, saboda ka kiyaye dokar Ubangiji Allahnka.

  9. Ta haka za ka yi nasara in ka mai da hankali ga kiyaye ƙa’idodi da dokokin da Ubangiji ya ba wa Musa saboda Isra’ila. Ka yi ƙarfin hali ka kuma ƙarfafa. Kada ka ji tsoro ko ka fid da zuciya.

  10. “Na sha wahala da yawa don in yi tanadi talentin dubu ɗari na zinariya, talenti miliyon na azurfa, ɗumbun tagulla da ƙarfe da suka wuce ƙirge da katako da dutse saboda haikalin Ubangiji. Za ka iya ƙara su.

  11. zinariya da azurfa, tagulla da ƙarfe, masu sana’a waɗanda suka wuce ƙirge. Yanzu ka fara aiki, Ubangiji kuma ya kasance tare da kai.”

  12. Ya ce musu, “Ba Ubangiji Allahnku yana tare da ku ba? Bai kuma ba ku hutu a kowane gefe ba? Gama ya ba da mazaunan ƙasar gare ni, ƙasar kuma ta Ubangiji ce da mutanensa.

  13. Yanzu fa sai ku sa zuciyarku da ranku ga neman Ubangiji Allahnku. Ku fara ginin wuri mai tsarki na Ubangiji Allah, don ku kawo akwatin alkawarin Ubangiji da kayayyaki masu tsarki na Allah a cikin haikalin da za a gina saboda Sunan Ubangiji.”

  14. Dawuda ya ce, “Cikin waɗannan, dubu ashirin da huɗu za su lura da aikin haikalin Ubangiji, dubu shida su zama manyan na ma’aikata da alƙalai.

  15. Dubu huɗu su zama matsaran ƙofofi, dubu huɗu kuma su yabi Ubangiji da kayayyakin bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe waɗanda na tanada saboda wannan manufa.”

  16. ’Ya’yan Amram maza su ne, Haruna da Musa. Haruna shi ne aka keɓe, shi da zuriyarsa har abada, don su tsarkake kayayyakin mafi tsarki, su miƙa hadayu a gaban Ubangiji, su yi hidima a gabansa su kuma furta albarku a cikin sunansa har abada.

  17. An ƙidaya aka kuma haɗa ’ya’yan Musa maza mutumin Allah a sashen kabilar Lawi.

  18. Waɗannan ne zuriyar Lawi bisa ga iyalansu, kawunan iyalai kamar yadda aka rubuta su a ƙarƙashin sunayensu aka kuma ƙirga kowa, wato, masu aikin da suke ’yan shekara ashirin da haihuwa ko fiye waɗanda suka yi hidima a cikin haikalin Ubangiji.

  19. Gama Dawuda ya ce, “Tun da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya ba da hutu ga mutanensa, ya kuma zo ya zauna a Urushalima har abada,

  20. Aikin Lawiyawa shi ne su taimaki zuriyar Haruna a hidimar haikalin Ubangiji; su lura da filaye da kuma ɗakunan da suke gefe, su tsarkake dukan kayayyaki masu tsarki, su kuma yi waɗansu ayyuka a gidan Allah.

  21. Su ne kuma za su tsaya kowace safiya su yi godiya, su kuma yabi Ubangiji. Za su kuma yi haka da yamma

  22. da kuma a duk sa’ad da aka miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a Asabbatai da bukukkuwan Sabon Wata da kuma a ƙayyadaddun bukukkuwa, za su yi hidima a gaban Ubangiji kullum bisa ga yawan da aka tsara da kuma a hanyar da aka tsara musu.

  23. A haka kuwa Lawiyawa suka yi ayyukansu don Tentin Sujada, don Wuri Mai Tsarki da kuma a ƙarƙashin ’yan’uwansu zuriyar Haruna, saboda hidimar haikalin Ubangiji.

  24. Aka karkasa su babu sonkai ta wurin jifa ƙuri’a, gama akwai manyan ma’aikatan wuri mai tsarki da manyan ma’aikatan Allah a cikin zuriyar Eleyazar da Itamar.

  25. Ga tsarin aikinsu na hidima sa’ad da suka shiga haikalin Ubangiji, bisa ga ƙa’idar da kakansu Haruna ya kafa, yadda Ubangiji, Allah na Isra’ila ya umarce shi.