Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Bawanka ya kashe zaki da beyar, wannan Bafilistin marar kaciya zai zama kamar ɗaya daga cikinsu, domin ya rena rundunar Allah mai rai.

  2. Ubangiji wanda ya cece ni daga kumbar zaki da kuma kumbar beyar, zai cece ni daga hannun wannan Bafilistin.” Shawulu ya ce wa Dawuda, “Je ka, Ubangiji yă kasance tare da kai.”

  3. Dawuda ya ce wa Bafilistin, “Kana zuwa ka yaƙe ni da māshi da takobi da kere, amma ni ina zuwa in yaƙe ka a cikin sunan Ubangiji Maɗaukaki, Allah na rundunar Isra’ila, wanda ka rena.

  4. Yau nan, Ubangiji zai bashe ka a hannuna, zan kuwa kashe ka, in datse kanka. Yau, zan ba da gawawwakin rundunar Filistiyawa ga tsuntsayen sama da namun jeji, da haka duniya za tă sani lalle akwai Allah a cikin Isra’ila.

  5. Duk waɗanda suka taru a nan za su san cewa ba da māshi ko takobi ne Ubangiji yake ceto ba, gama yaƙin nan na Ubangiji ne, shi kuwa zai bashe ku duka a hannuwanmu.”

  6. Kashegari, mugun ruhu daga Allah ya fāɗo wa Shawulu da tsanani. Yana annabci a gidansa, Dawuda kuwa yana bugan molo kamar yadda ya saba. Shawulu yana riƙe da māshi a hannunsa.

  7. Shawulu ya ji tsoron Dawuda don Ubangiji yana tare da shi, amma Ubangiji ya riga ya bar Shawulu.

  8. A kome da Dawuda ya yi yakan yi nasara gama Ubangiji yana tare da shi.

  9. Shawulu ya ce wa Dawuda, “Ga diyata Merab zan ba ka ka aura, kai dai ka yi mini aiki da himma, ka kuma yi yaƙe-yaƙen Ubangiji.” Saboda Shawulu ya ce wa kansa, “Ba zan ɗaga hannuna a kansa ba, Filistiyawa ne za su yi wannan.”

  10. Da Shawulu ya gane Ubangiji yana tare da Dawuda, ’yarsa Mikal kuma tana ƙaunarsa,

  11. Ya yi kasai da ransa sa’ad da ya kashe Bafilistin nan. Ubangiji ya ba wa dukan Isra’ila babban nasara, ka gani, ka kuma yi farin ciki. Don me za ka ci mutuncin amintaccen mutum kamar Dawuda ta wurin kashe shi ba tare da wani dalili ba?”

  12. Shawulu ya saurari Yonatan sai ya rantse ya ce, “Muddin Ubangiji yana a raye, ba za a kashe Dawuda ba.”

  13. Amma mugun ruhu daga Ubangiji ya sauko wa Shawulu yayinda yana zaune a cikin gidansa da māshi a hannunsa. Yayinda Dawuda yake bugan molo,

  14. Sai ya aiki mutane su je su kamo Dawuda, amma da suka ga ƙungiyar annabawa suna annabci tare da Sama’ila shugabansu a tsaye, sai Ruhun Allah ya sauko wa mutanen Shawulu, su ma suka fara yin annabci.

  15. Saboda haka Shawulu ya tafi Nayiwot a Rama, amma Ruhun Allah ya sauko masa, shi ma ya yi tafiya yana annabci har sai da ya isa Nayiwot.

  16. Yonatan ya ce, “Faufau, ba za ka mutu ba! Ka ji nan, mahaifina ba ya yin kome ba tare da ya shawarce da ni ba. Me ya sa ya ɓoye mini wannan? Ba zai yiwu ba.”

  17. Sai Dawuda ya rantse ya ce, “Mahaifinka ya san cewa, na sami tagomashi a gare ka, domin haka ba zai sanar maka da wannan ba, don kada yă baƙanta maka rai. Na rantse da Ubangiji, da kai kuma, taki ɗaya kaɗai ya rage tsakanina da mutuwa.”

  18. Kai kuma, ka nuna alheri ga bawanka, gama ka riga ka yi yarjejjeniya da ni a gaban Ubangiji, in kuwa na yi laifi ne sai ka kashe ni da kanka. Don me za ka bashe ni ga mahaifinka?”

  19. Sai Yonatan ya ce wa Dawuda, “Na yi rantse da Ubangiji, Allah na Isra’ila cewa war haka jibi, zan yi ƙoƙari in ji daga mahaifina, idan ya yi magana mai kyau game da kai, zan gaya maka.

  20. Amma in mahaifina ya sa zuciya yă cuce ka, Ubangiji yă hukunta ni da hukunci mai tsanani in ban gaya maka ba, in kuma sa ka ka tafi lafiya. Ubangiji yă kasance tare da kai kamar yadda ya kasance da mahaifina.

  21. Amma ka nuna mini alheri marar ƙarewa iri ta Ubangiji dukan rayuwata don kada a kashe ni.

  22. Kada kuma ka yanke alherinka ga iyalina ko da Ubangiji ya hallaka dukan maƙiyin Dawuda a duniya.”

  23. Saboda haka Yonatan ya yi yarjejjeniya da gidan Dawuda cewa Ubangiji yă kawo dukan maƙiyin Dawuda ga mutuwa.

  24. Sa’an nan zan aiki yaro in ce masa, ‘Je ka nemo kibiyoyin.’ In na ce masa, ‘Duba, kibiyoyin suna wannan gefen da kake, kawo su,’ sai ka fito, wato, tabbatacce muddin Ubangiji yana raye, ka tsira, ba wani hatsari.

  25. Amma in na ce wa yaron, ‘Duba, kibiyoyin suna gaba da kai,’ sai ka tafi, gama Ubangiji ya sallame ka.