Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Zobah: Its inhabitants mercenaries of the Ammonites against David

28 ayoyi · 5 fannoni

Ayoyi game da Its inhabitants mercenaries of the Ammonites against David

Tace bisa littafi
  1. Da Ammonawa suka gane cewa Dawuda ya ji fushi da su sosai saboda abin da suka yi, sai suka yi hayar sojojin ƙasar Arameyawa dubu ashirin daga Bet Rehob da Aram-Zoba, suka kuma yi hayar sarkin Ma’aka tare da mutum dubu ɗaya, suka kuma yi hayar maza dubu goma sha biyu daga Tob.

  2. Da jin haka, Dawuda ya tura Yowab da dukan sojojin yaƙi.

  3. Ammonawa suka fita suka ja dāgār yaƙi a ƙofar shiga birninsu, yayinda Aram-Zoba, da na Rehob, da mutane Tob, da kuma na Ma’aka, suka ja tasu dāgār a karkara.

  4. Yowab ya ga cewa an ja masa dāgār yaƙi gaba da baya; saboda haka sai ya zaɓi waɗansu shahararrun sojoji cikin Isra’ila, ya sa su gabza da Arameyawa.

  5. Ya sa sauran mutanen a ƙarƙashin Abishai ɗan’uwansa, ya sa su gabza da Ammonawa.

  6. Yowab ya ce, “In Arameyawa suka fi ƙarfina, sai ku kawo mini gudummawa; amma in Ammonawa suka fi ƙarfinku, sai mu kawo muku gudummawa.

  7. Ku yi ƙarfin hali, mu kuma yi yaƙi da ƙarfin zuciya saboda mutanenmu da kuma birane Allahnmu. Ubangiji zai yi abin da yake da kyau a idanunsa.”

  8. Sa’an nan Yowab da rundunar da take tare da shi suka ci gaba don su gabza da Arameyawa, Arameyawa kuwa suka gudu a gabansa.

  9. Da Ammonawa suka ga Arameyawa suna gudu, sai su ma suka ruga da gudu a gaban Abishai, suka shiga cikin birni. Sa’an nan Yowab ya komo Urushalima daga wurin yaƙin da ya yi da Ammonawa.

  10. Bayan Arameyawa suka ga Isra’ila ta ci su da yaƙi, sai suka sāke tattara kansu.

  11. Hadadezer sarkin Zoba ya aika a kawo Arameyawan da suke ƙetaren Kogin Yuferites. Suka iso Helam a ƙarƙashin shugabancin Shobak, shugaban dukan sojojin Hadadezer.

  12. Da aka gaya wa Dawuda wannan, sai ya tattara dukan Isra’ila, ya ƙetare Urdun, ya je Helam. Arameyawa suka ja dāgār yaƙinsu, suka kara da Dawuda.

  13. Amma Arameyawa suka gudu a gaban Isra’ila, Dawuda kuwa ya kashe mahayan keken yaƙinsu ɗari bakwai, da sojojin ƙasa dubu arba’in. Ya bugi Shobak, shugaban ƙungiyar sojansu ya kuwa mutu a can.

  14. Sa’ad da dukan sarakuna waɗanda suke abokan tarayya na Hadadezer suka ga Isra’ila sun ci su da yaƙi, sai suka yi sulhu da Isra’ilawa, suka kuma zama bayinsu. Wannan ya sa Arameyawa suka ji tsoron ƙara kai wa Ammonawa gudummawa.

  15. Sa’ad da Ammonawa suka gane cewa sun zama abin wurin a kafan hancin Dawuda, Hanun da Ammonawa suka aika da talenti dubu na azurfa don su yi haya da kekunan yaƙi da mahayan kekunan yaƙi daga Aram-Naharayim, Aram Ma’aka da Zoba.

  16. Suka yi hayar kekunan yaƙi da mahayan kekunan yaƙi dubu talatin da biyu, da kuma sarkin Ma’aka tare da mayaƙansa, waɗanda suka zo suka kafa sansani kusa da Medeba, yayinda Ammonawa suka tattaru daga garuruwansu suka fita yaƙi.

  17. Da jin haka, Dawuda ya aiki Yowab tare da dukan mayaƙa masu yaƙi.

  18. Ammonawa suka fito suka ja dāgā a ƙofar birninsu, yayinda sarakunan da suka zo, su kansu suka ware suna a fili.

  19. Yowab ya ga cewa akwai dāgā a gabansa da bayansa; sai ya zaɓi waɗansu mayaƙa mafi kyau a Isra’ila ya sa su a kan Arameyawa.

  20. Ya sa sauran mutanen a ƙarƙashin kulawar Abishai ɗan’uwansa, aka sa a kan Ammonawa.

  21. Yowab ya ce, “In Arameyawa suka fi ni ƙarfi, sai ka kawo mini ɗauke da ni; amma in Ammonawa sun fi ka ƙarfi, sai in kawo maka ɗauke.

  22. Ka yi ƙarfin hali bari mu yi yaƙi da jaruntaka saboda mutanenmu da biranen Allahnmu. Ubangiji zai yi abin da ya ga ya yi masa kyau.”

  23. Sai Yowab da ƙungiyoyin mayaƙan da suke tare da shi suka matso don su yi yaƙi da Arameyawa, Arameyawan kuwa suka gudu a gabansa.

  24. Sa’ad da Ammonawa suka ga Arameyawa suna gudu, sai su ma suka guda a gaban ɗan’uwansa Abishai suka shiga cikin birni. Sai Yowab ya koma Urushalima.

  25. Bayan Arameyawa suka ga cewa Isra’ila sun ci su da yaƙi, sai suka aiki ’yan aika suka sa aka kawo Arameyawan da suke hayen Kogi waɗanda Shobak shugaban mayaƙan Hadadezer yake shugabanta.