Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Witness: To the transfer of land

25 ayoyi · 10 fannoni

Ayoyi game da To the transfer of land

  1. Sa’an nan Ibrahim ya kawo kuka ga Abimelek game da rijiyar ruwan da bayin Abimelek suka ƙwace.

  2. Sai Abimelek ya ce, “Ban san wanda ya yi wannan ba. Ba ka faɗa mini ba, ban kuwa taɓa ji ba, sai yau.”

  3. Sai Ibrahim ya kawo tumaki da shanu ya ba wa Abimelek, sai su biyun suka yi yarjejjeniya.

  4. Ibrahim ya ware ’yan raguna bakwai daga cikin garke,

  5. sai Abimelek ya ce wa Ibrahim, “Mene ne ma’anar ’yan raguna bakwai da ka keɓe?”

  6. Ibrahim ya amsa ya ce, “Ka karɓi waɗannan ’yan tumaki bakwai daga hannuna a matsayin shaida cewa ni ne na haƙa wannan rijiya.”

  7. Ya ce, “A’a, ranka yă daɗe, ka ji ni, na ba ka filin, na kuma ba ka kogon da yake cikinsa. Na ba ka shi a gaban mutanena. Ka binne mataccenka.”

  8. Ibrahim ya yarda da sharuɗan Efron, sai ya auna masa farashin da ya faɗa a kunnuwan Hittiyawa, shekel ɗari huɗu na azurfa, bisa ga ma’aunin da ’yan kasuwa suke amfani da shi a lokacin.

  9. Ta haka filin Efron a Makfela kusa da Mamre, wato, filin da kogon a cikinsa, da kuma dukan itatuwan da suke cikin iyakoki filin, aka

  10. ba wa Ibrahim a matsayin mallakarsa a gaban dukan Hittiyawa waɗanda suka zo ƙofar birnin.

  11. Ana cikin haka Bowaz ya haura zuwa ƙofar gari ya tafi ya zauna a can. Sa’ad da dangi mai fansan da ya yi zance ya iso, Bowaz ya ce, “Zo nan abokina ka zauna.” Saboda haka ya ratso ya zauna.

  12. Bowaz kuwa ya kira dattawa guda goma na garin ya ce, “Ku zauna a nan,” suka kuwa zauna.

  13. Sa’an nan ya ce wa dangin nan mai fansa, “Na’omi, wadda ta dawo daga Mowab, tana so ta sayar da filin da yake na ɗan’uwanmu Elimelek.

  14. Na ga ya kamata in jawo hankalinka ga batun in kuma ba da shawara ka saye shi a gaban waɗannan da suke zazzaune a nan da kuma a gaban dattawan jama’a. In kana so ka fanshe shi, to, sai ka yi. Amma in ba za ka yi ba, sai ka faɗa mini, don in sani. Gama babu wani mai izinin yin haka sai kai, ni ne kuwa na biye.” Sai ya ce, “Zan fansa.”

  15. Sa’an nan Bowaz ya ce, “A ranar da ka saya filin daga Na’omi da kuma daga Rut mutuniyar Mowab, ka sayi gwauruwar marigayin nan, domin ka riƙe sunan marigayin da kuma kayansa.”

  16. Da jin haka, sai dangin nan mai fansa ya ce, “To, ba zan iya fanshe shi ba don kada in yi wa nawa mallakar rauni. Za ka iya fanshe shi wa kanka. Ni dai ba zan iya ba.”

  17. (To, a kwanakin can a Isra’ila, domin a tabbatar da fansa da kuma musayar da mallaka, mutum zai cire takalminsa ya ba wa ɗayan. Wannan ita ce hanyar tabbatar da al’amarin a hukumance a cikin Isra’ila.)

  18. Saboda haka dangin nan mai fansa ya ce wa Bowaz, “Saye shi wa kanka.” Sai ya cire takalminsa.

  19. Sa’an nan Bowaz ya yi shela wa dattawa da kuma dukan mutane, “A yau ku ne shaidu cewa na saya daga Na’omi dukan mallakar Elimelek, Kiliyon da kuma Malon.

  20. saboda haka sai na saye filin a Anatot daga hannun Hananel yaron ɗan’uwan mahaifina na kuma auna masa shekel goma sha bakwai na azurfa.

  21. Na sa hannu a takarda, na buga hatimi na liƙe, na sami shaidu na kuwa auna shekel a ma’auni.

  22. Na ɗauki takardar ciniki, takardar da aka rubuta sharuɗan a ciki, da kuma takardar da ba a liƙe ba,

  23. na kuma ba wa Baruk ɗan Neriya, ɗan Masehiya, wannan takarda a gaban Hananel yaron ɗan’uwan mahaifina da kuma a gaban shaidun da suka sa hannu a takardan ciniki da kuma a gaban dukan Yahudawan da suke zaune a sansanin matsaran.

  24. Ko da yake za a ba da birnin ga Babiloniyawa, kai, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ka ce mini, ‘Saye fili da azurfa ka kuma sa a shaida cinikin.’ ”

  25. Za a sayi filaye da azurfa, a kuma sa hannu a takardan ciniki, a liƙe a kuma shaida a yankin Benyamin, a ƙauyukan kewayen Urushalima, a garuruwan Yahuda da kuma a garuruwan ƙasar tudu, na yammancin gindin dutse da na Negeb, domin zan maido da wadatarsu, in ji Ubangiji.”