Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Tribes of Israel: Settled on east side of Jordan

16 ayoyi · 21 fannoni

Ayoyi game da Settled on east side of Jordan

  1. Cikin ƙasar da muka kwasa a lokacin, na ba wa mutanen Ruben da mutanen Gad yankin arewa na Arower ta Kwarin Arnon, haɗe da rabin ƙasar tudu ta Gileyad, tare da biranenta.

  2. Sai kuma na ba wa rabin kabilar Manasse sauran rabin ƙasar tudu ta Gileyad da kuma dukan Bashan, masarautar Og (Wato, dukan yankin ƙasan nan na Argob a Bashan da dā ake kira ƙasar Refahiyawa.

  3. Yayir na zuriyar Manasse ya karɓi dukan yankin ƙasar Argob a Bashan har zuwa iyakar Geshurawa da Ma’akatiyawa. Sai ya kira ƙauyukan wurin da sunansa, Hawwot Yayir.)

  4. Na kuma ba da Gileyad ga Makir.

  5. Amma ga mutanen Ruben da mutanen Gad, na ba da yankin da ya tashi daga Gileyad, ya gangara zuwa Kwarin Arnon (tsakiyar kwarin kuwa shi ne iyaka) ya fita zuwa Kogin Yabbok, wanda yake shi ne iyakar Ammonawa.

  6. Iyakarsa daga yamma kuwa shi ne Urdun a Araba, daga Kinneret zuwa Tekun Araba (wato, Tekun Gishiri) a gangaren gindin Dutsen Fisga wajen gabas.

  7. Gefen Urdun shi ne iyakar mutanen Ruben. Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne gādon mutanen Ruben, bisa ga iyalansu.

  8. Ga abin da Musa ya ba kabilar Gad, bisa ga iyalansu.

  9. Yankin ƙasarsu ya ƙunshi Yazer, da dukan garuruwan Gileyad, da rabin ƙasar Ammonawa har zuwa Arower kusa da Rabba,

  10. da kuma daga Heshbon zuwa Ramat Mizfa da Betonim, da kuma daga Mahanayim zuwa sashen Debir,

  11. kuma a cikin kwari, Bet-Haram, Bet-Nimra, Sukkot da Zafon da kuma sauran masarautar Sihon sarkin Heshbon (gabashin Urdun, abin da ya kama har zuwa ƙarshen Tekun Kinneret).

  12. Waɗannan garuruwan da ƙauyukansu duka, gādon mutanen Gad ne, bisa ga iyalansu.

  13. Ga abin da Musa ya ba rabin kabilar Manasse, wato, wa rabin zuriyar Manasse, bisa ga iyalansu.

  14. Abin da ya miƙe daga Mahanayim haɗe da dukan Bashan, da gefen masarautar Og sarkin Bashan, da dukan garuruwan Yayir guda sittin da suke a Bashan,

  15. da rabin Gileyad, da Ashtarot, Edireyi (biranen sarki Og a Bashan). Wannan shi ne rabon da zuriyar Makir ɗan Manasse suka samu, domin rabin ’ya’yan Makir maza, bisa ga iyalansu.

  16. Waɗannan su ne rabon gādon da Musa ya yi lokacin da suke cikin filayen Mowab a hayin gabashin Urdun kusa da Yeriko.