Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Tribes of Israel: Total strength of, on leaving Egypt

5 ayoyi · 21 fannoni

Ayoyi game da Total strength of, on leaving Egypt

  1. Isra’ilawa suka kama tafiya daga Rameses zuwa Sukkot. Akwai maza dubu ɗari shida da suke tafiya da ƙafa, ban da mata da yara.

  2. Waɗannan su ne mazan da Musa da Haruna, tare da shugabanni goma sha biyun nan na Isra’ila suka ƙidaya, kowa a madadin iyalinsa.

  3. Dukan Isra’ilawan da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, an ƙidaya su bisa ga iyalansu.

  4. Jimillar kuwa ita ce mutum 603,550.

  5. Waɗannan su ne Isra’ilawan da aka a ƙidaya bisa ga iyalansu. Dukansu da suke a sansani, mutane 603,550 ne.