Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Tribe Of Zebulun: Bounds of their inheritance

7 ayoyi · 23 fannoni

Ayoyi game da Bounds of their inheritance

  1. Ƙuri’a ta uku ta fāɗa a kan Zebulun bisa ga iyalansu. Iyakar ƙasarsu ta gādo ta kai har Sarid.

  2. Ta nufi yamma zuwa Marala, ta taɓa Dabbeshet, ta wuce zuwa rafin da yake kusa da Yokneyam.

  3. Daga Sarid, ta juya gabas zuwa harabar Kislot Tabor, ta kuma wuce zuwa Daberat har zuwa Yafiya.

  4. Sa’an nan ta ci gaba, ta yi gabas zuwa Gat-Hefer da Et Kazin; ta ɓulla a Rimmon, ta juya zuwa Neya.

  5. A can ne iyakar ta kewaya zuwa Hannaton, sa’an nan ta ƙarasa a Kwarin Ifta El.

  6. Zebulun ta ƙunshi garuruwa goma sha biyu da ƙauyukansu. Garuruwan sun haɗa da Kattat, Nahalal, Shimron, Idala da Betlehem.

  7. Garuruwan nan da ƙauyukansu su ne gādon da kabilar Zebulun ta samu, bisa ga iyalansu.