Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Pharisees: Zealous of tradition

6 ayoyi · 42 fannoni

Ayoyi game da Zealous of tradition

  1. (Farisiyawa da dukan Yahudawa ba sa cin abinci, sai sun wanke hannuwa sarai tukuna, yadda al’adun dattawa suka ce.

  2. Saboda haka, Farisiyawa da malaman dokoki suka tambayi Yesu, suka ce, “Don me almajiranka ba sa bin al’adun dattawa, a maimakon haka suna cin abinci da hannuwa marasa tsabta?”

  3. Ya amsa ya ce, “Daidai ne Ishaya ya yi annabci game da ku munafukai; kamar yadda yake a rubuce cewa, “ ‘Waɗannan mutane da baki suke girmama ni, amma zukatansu sun yi nesa da ni.

  4. A banza suke mini sujada, koyarwarsu, dokokin mutane ne kawai.’

  5. Kun yar da umarnan Allah, kuna bin al’adun mutane.”

  6. Na ci gaba a cikin Yahudanci fiye da yawancin Yahudawan da suke tsarana, na kuma yi ƙwazo ƙwarai ga bin al’adun kakannina.