Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Thanksgiving: The heavenly host engaged in

5 ayoyi · 57 fannoni

Ayoyi game da The heavenly host engaged in

  1. Duk lokacin da halittu masu ran nan suka rera ɗaukaka, girma da kuma godiya ga wannan wanda yake zaune a kan kursiyin da kuma wanda yake mai rai har abada abadin,

  2. Dukan mala’iku suna tsaye kewaye da kursiyin da kuma kewaye da dattawan tare da halittu huɗun nan masu rai. Suka fāɗi da fuskokinsu ƙasa a gaban kursiyin suka kuma yi wa Allah sujada,

  3. suna cewa, “Amin! Yabo da ɗaukaka, da hikima da godiya da girma da iko da ƙarfi sun tabbata ga Allahnmu har abada abadin. Amin!”

  4. Sai dattawan nan ashirin da huɗu da suke zaune a kursiyoyinsu a gaban Allah, suka fāɗi da fuskokinsu a ƙasa suka kuma yi wa Allah sujada,

  5. suna cewa, “Muna maka godiya ya Ubangiji Allah, Maɗaukaki, wanda yake a yanzu, shi ne kuma a dā, domin ka karɓi ikonka mai girma ka kuma fara mulki.