Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sihon

27 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Isra’ila suka aiki manzanni wurin Sihon sarkin Amoriyawa su ce,

  2. “Ka bari mu ratsa ta ƙasarka. Ba za mu shiga wata gona ba, ba za mu kuma shiga gonar inabi, ko mu sha ruwa daga wata rijiya ba. Za mu bi ta babbar hanyar sarki, har mu fita ƙasarka.”

  3. Amma Sihon bai bar Isra’ila su ratsa ta yankinsa ba. Sai ya tara dukan sojojinsa, suka fita zuwa cikin hamada, su yaƙi Isra’ila. Da ya kai Yahaz, sai ya yaƙi Isra’ila.

  4. Isra’ila fa suka kashe shi da takobi, suka ƙwace ƙasarsa, tun daga kogin Arnon har zuwa kogin Yabbok, zuwa kan iyakar Ammonawa kawai, gama sun yi wa iyakansu katanga.

  5. Isra’ila suka ci dukan biranen Amoriyawa, suka kuma zauna a cikinsu, haɗe da babban birnin Heshbon da dukan ƙauyukanta.

  6. Sihon sarkin Amoriyawa ya yi mulkin Heshbon, bayan ya ci sarkin Mowab na dā da yaƙi, ya kuma ƙwace dukan ƙasarsa har zuwa arewancin kogin Arnon.

  7. Shi ya sa Amoriyawa suka rubuta wannan waƙa game da Heshbon suka ce, “Ku zo mu sāke gina Heshbon, birnin Sihon.

  8. “Mayaƙansa sun fito kamar harshen wuta suka ƙone birnin Ar na Mowab suna hallaka ’yan ƙasar tuddan Arnon.

  9. Kaitonki, Mowab! Gunkinki Kemosh ya yashe mutanenki; aka kuma kama su, aka kai su bauta wajen Sihon sarkin Amoriyawa.

  10. “Amma mun tumɓuke su, mun hallaka garuruwan Heshbon har zuwa Dibon. Mun ragargaza su har zuwa Nofa wanda ya miƙe zuwa Medeba.”

  11. “Ku fito yanzu ku ƙetare Kwarin Arnon. Duba, na ba da Sihon mutumin Amoriyawa a hannunku, na kuma ba da sarkin Heshbon da ƙasarsa. Ku fara mallake ta, ku kuma yi yaƙi da shi.

  12. A wannan rana zan fara sa tsoro da fargabanku a kan dukan al’ummai, a ƙarƙashin sama. Za su ji labarinku, za su yi rawan jiki, su kuma damu saboda ku.”

  13. Daga hamadar Kedemot, na aiki ’yan saƙo zuwa wurin Sihon sarkin Heshbon, a kan ina neman zaman lafiya, ina cewa,

  14. “Bari mu wuce cikin ƙasarka. Za mu bi ta kan hanya ne kaɗai; ba za mu ratse dama ko hagu ba.

  15. Ka sayar mana da abincin da za mu ci, da kuma ruwan da za mu sha a farashinsu na azurfa. Ka dai bar mu mu wuce ta ƙasarka kawai,

  16. kamar yadda zuriyar Isuwa, waɗanda suke zaune a Seyir, da Mowabawa, waɗanda suke zaune a Ar, suka yardar mana, gama muna so mu ƙetare Urdun zuwa ƙasa wadda Ubangiji, Allahnmu yake ba mu.”

  17. Amma Sihon sarkin Heshbon ya ƙi yă bar mu mu wuce a ciki. Gama Ubangiji Allahnku ya sa ruhunsa ya taurare don yă ba da shi a hannuwanku kamar yadda ya yi yanzu.

  18. Ubangiji ya ce mini, “Duba, na fara ba da Sihon da ƙasarsa gare ku. Yanzu ku fara cinta, ku kuma mallake ƙasarsa.”

  19. Sa’ad da Sihon da dukan sojojinsa suka fito don su sadu da mu, a yaƙi, a Yahaz,

  20. sai Ubangiji Allahnmu ya ba da shi gare mu, muka kuwa buga shi tare da ’ya’yansa maza da kuma dukan sojojinsa.

  21. A wannan lokaci mun ci dukan biranensa, muka kuma hallaka su, maza, mata da kuma yara. Ba mu bar wani da rai ba.

  22. Amma muka washe, muka kuma kwasa shanu da kuma ganima daga biranen wa kanmu.

  23. Ubangiji Allahnmu ya taimake mu muka ci Arower wadda take a gefen Kwarin Arnon, da garin da yake a cikin kwarin, har zuwa Gileyad. Babu garin da ya gaggare mu.

  24. Amma bisa ga umarnin Ubangiji Allahnmu, ba ku yi kusa da wata ƙasar Ammonawa, ko ƙasar da take gefen kwarin kogin Yabbok, ko kuwa wadda take kewaye da birane cikin tuddai ba.

  25. Ubangiji ya ce mini, “Kada ka ji tsoronsa, gama na riga na miƙa shi da dukan mayaƙansa da kuma ƙasarsa gare ka. Yi masa abin da ka yi wa Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulkin Heshbon.”