Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Shoe

16 ayoyi · 9 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. cewa ba zan karɓi kome da yake naka ba, ko zare ko maɗaurin takalma, don kada ka ce, ‘Na azurta Abram.’

  2. Allah ya ce, “Kada ka zo kusa, tuɓe takalmanka, gama inda kake tsaye, wuri ne mai tsarki.”

  3. sai gwauruwan nan, matar ɗan’uwansa tă haura wurinsa a gaban dattawa, tă tuɓe takalminsa guda, ta tofa masa miyau a fuska, tă ce, “Haka za a yi ga mutumin da zai ƙi kafa gidan ɗan’uwansa.”

  4. Shekaru arba’in da na jagorance ku cikin hamada, tufafinku ba su yage ba, haka kuwa takalman da suke a ƙafafunku.

  5. Madogaran ƙofofinka za su zama ƙarfe da tagulla, ƙarfinka kuma zai zama daidai da kwanakinka.

  6. Shugaban rundunar sojojin Ubangiji ya amsa ya ce, “Ka cire takalmanka, gama wurin da kake tsaye, mai tsarki ne.” Sai Yoshuwa ya cire takalmansa.

  7. (To, a kwanakin can a Isra’ila, domin a tabbatar da fansa da kuma musayar da mallaka, mutum zai cire takalminsa ya ba wa ɗayan. Wannan ita ce hanyar tabbatar da al’amarin a hukumance a cikin Isra’ila.)

  8. Saboda haka dangin nan mai fansa ya ce wa Bowaz, “Saye shi wa kanka.” Sai ya cire takalminsa.

  9. Babu ko ɗayansu da ya gaji ko ya yi tuntuɓe, babu ko ɗaya da ya yi gyangyaɗi ko barci; babu abin ɗamarar da ya kunce a gindi, ba igiyar takalmin da ta tsinke.

  10. Na rufe ki da rigar da aka yi wa ado na kuma sa miki takalman fata. Na sa miki riga ta lilin mai kyau na kuma rufe ki da riguna masu tsada.

  11. Ka yi nishi shiru; kada ka yi makoki saboda matacciyar. Ka naɗa rawaninka ka kuma sa takalmanka a ƙafa; kada ka rufe sashen fuskarka daga ƙasa ko ka ci abincin da masu kuka sukan ci.”

  12. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Isra’ila, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Don sun sayar da adalai waɗanda suka kāsa biyan bashinsu. Sun kuma sayar da matalauta waɗanda bashinsu bai ma kai ko kuɗin bi-labi ba.

  13. mu sayi matalauta da azurfa masu bukata kuma da takalmi, mu sayar da alkamar haɗe da yayi.

  14. Wannan kuwa shi ne saƙonsa, “A bayana, wanda ya fi ni iko yana zuwa, ban kuwa isa in sunkuya in kunce igiyar takalmansa ba.

  15. Yohanna ya amsa musu duka ya ce, “Ina muku baftisma da ruwa. Amma wani wanda ya fi ni iko yana zuwa, ban ma isa in kunce igiyar takalmansa ba. Shi zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da wuta kuma.

  16. “Sa’an nan Ubangiji ya ce masa, ‘Ka cire takalmanka; wurin da kake tsayen nan mai tsarki ne.