Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Shewbread

34 ayoyi · 26 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Ka yi tebur da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kuma kamu ɗaya da rabi.

  2. Ka dalaye shi da zinariya zalla ka kuma yi masa ado kewaye da gurun zinariya.

  3. Ka yi dajiya mai fāɗin tafin hannu, ka kuma yi wa dajiyar ado da gurun zinariya.

  4. Ka yi zoban zinariya huɗu domin teburin, ka daure su a kusurwoyi huɗu, inda ƙafafu huɗun suke.

  5. Zoban za su kasance kusa da dajiyar don riƙe sandunan da za a yi amfani don ɗaukar teburin.

  6. Ka yi sandunan da itacen ƙirya, ka dalaye su da zinariya, da sandunan ne za ku riƙa ɗaukan teburin.

  7. Da zinariya zalla kuma za ka yi farantansa, da kwanoninsa na tuya, da butocinsa, da kwanoninsa domin zuban hadayu.

  8. Ka sa burodin Kasancewa a kan wannan tebur, yă kasance a gabana kullum.

  9. Musa ya sa teburin a Tentin Sujada, a gefen arewa na tabanakul waje da labulen.

  10. Ya shirya burodin a kai a gaban Ubangiji, yadda Ubangiji ya umarce shi.

  11. “Ɗauki gari mai laushi a gasa dunƙulen burodi goma sha biyu, a yi amfani da humushi biyu na garwan gari don kowace burodi.

  12. A shirya su jeri biyu, guda shida a kowane jeri a kan teburin da aka yi da zinariya zalla, a gaban Ubangiji.

  13. Za a zuba turare a kowane layin dunƙulen burodin don yă kasance abin tunawa a bisa burodin. Turaren zai ƙone a madadin burodin don yă zama kamar hadayar da aka miƙa da wuta ga Ubangiji.

  14. Za a shirya wannan gurasa a gaban Ubangiji kowane Asabbaci, a madadin Isra’ilawa a matsayin madawwamin alkawari.

  15. Wannan burodin zai zama na Haruna da ’ya’yansa maza, waɗanda za su ci a tsattsarkan wuri, gama sashe ne mafi tsarki na rabonsu na kullum na hadayar da aka yi da wuta ga Ubangiji.”

  16. “A bisa teburin Burodin Ajiyewa, za su shimfiɗa zane mai ruwan shuɗi, a kansa kuma su sa farantai, kwanoni da manyan kwanoni, da tuluna don hadayun sha; da burodin da zai ci gaba da kasancewa a kansa.

  17. Amma firist ya ce wa Dawuda, “Ba ni da burodi iri na kowa da kowa, sai dai akwai burodin da aka tsarkake. Za ka iya ɗauka ku ci idan mutanenka ba su kwana da mata ba.”

  18. Dawuda ya ce, “Lalle ne a keɓe muke daga mata. Mutanena sukan keɓe kansu a koyaushe suka tashi ’yar tafiya, balle fa a yau!”

  19. Don haka firist ya ba shi keɓaɓɓen burodi, tun da yake babu wani burodi a can sai dai burodin Kasancewa da aka cire daga gaban Ubangiji, aka sa burodi mai zafi a maimakon wanda aka cire a ranar.

  20. Waɗansu ’yan’uwansu Kohatawa ne suke lura da shiryawa burodin da ake kaiwa a tebur a kowane Asabbaci.

  21. Su ne za su lura da burodin da aka ajiye a tebur, lallausan gari don hadaya ta gari, waina marar yisti, toyawa da kwaɓawa, da kuma dukan awon yawa da kuma girman abubuwa.

  22. Yanzu ina shirin ginin haikali domin Sunan Ubangiji Allahna, in kuma keɓe shi gare shi don ƙona turare mai ƙanshi a gabansa, don kuma ajiyar burodi mai tsarki kullum, da kuma don miƙa hadayun ƙonawa kowace safiya, kowace yamma, da a Asabbatai da Sababbin Wata, da kuma a ƙayyadaddun bukukkuwan Ubangiji Allahnmu. Wannan dawwammamiyar farilla ce don Isra’ila.

  23. “Mun ɗauka hakkin bin umarnai na ba da kashi ɗaya bisa uku na shekel kowace shekara don hidimar gidan Allahnmu.

  24. Za mu tanada burodin da ake ajiye a kan tebur; za mu ba da hadayun hatsi da hadayun ƙonawa na kullum; za mu ba da hadayun Asabbatai, da na bukukkuwan Sabon Wata da na bukukkuwan da aka ƙayyade; za mu ba da hadayu masu tsarki; za mu ba da hadayun zunubi don a yi kafara domin Isra’ila; mu kuma ba da abubuwan da ake bukata dukan domin ayyukan gidan Allahnmu.

  25. Sai ya amsa ya ce, “Ba ku karanta abin da Dawuda ya yi ba ne sa’ad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa?