Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Salt: Salt Sea

6 ayoyi · 29 fannoni

Ayoyi game da Salt Sea

  1. Dukan waɗannan sarakuna na bayan nan suka haɗa kai a Kwarin Siddim (Teku Gishiri).

  2. Sa’an nan tă gangara ta Urdun, tă ƙarasa a Tekun Gishiri. “ ‘Wannan za tă zama ƙasarku, tare da iyakokinta a kowane gefe.’ ”

  3. Iyakarsa daga yamma kuwa shi ne Urdun a Araba, daga Kinneret zuwa Tekun Araba (wato, Tekun Gishiri) a gangaren gindin Dutsen Fisga wajen gabas.

  4. sai ruwan da yake gangarowa ya tsaya, ya tattaru a wuri ɗaya ya yi tudu daga nan har zuwa wani garin da ake kira Adam kusa da Zaretan, ruwan da yake gangarowa zuwa Tekun Araba (Tekun Gishiri) kuma ya yanke gaba ɗaya. Sai mutane suka ƙetare kusa da Yeriko.

  5. Ya kuma yi mulki a kan gabashin Araba daga tekun Kinneret zuwa Tekun Araba (wato, Tekun Gishiri), zuwa Bet-Yeshimot da kuma kudu zuwa gangaren dutsen Fisga.

  6. Iyakarsu a kudanci ta tashi tun daga kurewar kudu na Tekun Gishiri,