Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Purification

100 ayoyi · 13 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Zai yi wanka a tsattsarkan wuri yă sa rigunarsa na kullum. Sa’an nan zai fita yă miƙa hadaya ta ƙonawa domin kansa da hadaya ta ƙonawa domin mutane, don yă yi kafara domin kansa da kuma domin mutane.

  2. “Dole mutumin da ya saki akuya na azazel yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka; bayan haka zai iya shiga sansani.

  3. Dole mutumin da ya ƙone su yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, bayan haka zai iya shiga sansani.

  4. “ ‘Kowa, ko haifaffe ɗan ƙasa ko baƙo, da ya ci wani abin da aka sami a mace, ko naman jeji ya yayyage, dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma; sa’an nan zai tsarkake.

  5. “Faɗa musu cewa, ‘Don tsararraki masu zuwa, in wani zuriyarku ya ƙazantu, duk da haka ya kusaci tsarkakakku hadayun da Isra’ilawa suka keɓe ga Ubangiji, dole a raba wannan mutum daga gabana. Ni ne Ubangiji.

  6. “Keɓe Lawiyawa daga sauran Isra’ilawa, ka tsarkake su.

  7. Ga yadda za ka tsarkake su, ka yayyafa musu ruwan tsarkakewa; ka sa su aske jikunansu duka su kuma wanke tufafinsu, ta haka za su tsarkake kansu.

  8. Lawiyawa suka tsarkake kansu, suka kuma wanke tufafinsu. Sai Haruna ya miƙa su kamar hadaya ta kaɗawa a gaban Ubangiji, ya kuma yi kafara saboda su don yă tsarkake su.

  9. Bayan haka, dole firist yă wanke rigunarsa, yă kuma yi wanka. Sa’an nan zai iya shiga cikin sansani, amma zai kasance da ƙazanta har yamma.

  10. Dole mutumin da ya ƙone ta yă wanke rigunarsa, yă kuma yi wanka, shi ma zai kasance da ƙazanta har yamma.

  11. Duk wanda ya taɓa gawar wani, bai kuma tsarkake kansa ba, ya ƙazantar da tabanakul na Ubangiji ke nan. Dole a ware wannan mutum daga cikin Isra’ilawa. Gama ba a yayyafa ruwan tsabtaccewa a kansa ba; ya ƙazantu, ya kasance da ƙazanta ke nan.

  12. “Ga wanda ya ƙazantu kuwa, a ɗiba toka daga hadaya ta ƙonawa ta tsarkakewa, a zuba a cikin tulu, sa’an nan a zuba ruwa mai gudu a kansu.

  13. Sa’an nan wanda yake tsarkakakke, zai ɗauki hizzob yă tsoma a ruwa, yă yayyafa a tentin da dukan kayayyakinsa, da kuma a kan mutanen da suke wurin. Dole kuma yă yayyafa ruwan a kan duk wanda ya taɓa ƙashin mutu, ko kabari, ko kuma wanda aka kashe, ko wanda ya yi mutuwa ta Allah.

  14. A rana ta uku, da ta bakwai kuma mai tsarkakewa zai yayyafa wa marar tsarkin ruwa, a rana ta bakwai kuma yă tsarkake shi. Wanda aka tsarkaken kuwa, dole yă wanke rigunarsa, yă kuma yi wanka da yamma, zai kuma tsarkaka.

  15. Amma in wanda yake da ƙazanta bai tsarkake kansa ba, dole a ware shi daga cikin jama’a, domin ya ƙazantar da wuri mai tsarki na Ubangiji. Ba a yayyafa masa ruwa na tsarkakewa ba, ya zama da ƙazanta.

  16. Wannan za tă zama musu dawwammamiyar farilla. “Mutumin da ya yayyafa ruwa na tsarkakewa, shi ma dole yă wanke rigarsa. Duk wanda kuma ya taɓa ruwan tsarkakewa, zai kasance da ƙazanta har yamma.

  17. “Dukanku da kuka kashe mutum, ko kuka taɓa wani da aka kashe, dole ku kasance a bayan sansani har kwana bakwai. A rana ta uku da rana ta bakwai dole ku tsabtacce kanku da kuma bayinku.

  18. Ku tsarkake kowace taguwa da kuma kome da aka yi da fata, da gashin akuya, ko kuwa itace.”

  19. Sa’an nan Eleyazar firist, ya ce wa sojojin da suka je yaƙi, “Wannan ita ce ƙa’idar da Ubangiji ya ba wa Musa.

  20. Zinariya, azurfa, tagulla, baƙin ƙarfe, kuza, darma

  21. da dukan abin da wuta ba ta iya ci, dole yă shiga wuta sa’an nan zai zama da tsabta. Amma dole a kuma tsarkake ta da ruwan tsarkakewa. Duk abin da wuta za tă iya ci, dole a shigar da ita a ruwan tsarkakewa.

  22. A rana ta bakwai za ku wanke tufafinku, sa’an nan za ku tsarkaka, bayan haka ku shigo sansani.”

  23. Sa’an nan dukan dattawan garin da yake kurkusa da gawar za su wanke hannuwansu a bisa karsanan da aka karye wuyar a kwarin,

  24. Sa’an nan ya yi daruna goma don wanki ya sa biyar a gefen kudu, biyar kuma a gefen arewa. A cikinsu kayan da za a yi amfani don ɗauraye hadayun ƙonawa, amma firistoci suna amfani da ƙaton kwano mai suna Teku don wanki.

  25. Na wanke hannuwana cikin rashin laifi, ina yawo a bagadenka Ya Ubangiji,