Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Palaces

48 ayoyi · 36 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Bari wurinsu yă zama kufai; kada ka bar wani yă zauna a tentunansu.

  2. Ya gina wurinsa mai tsarki kamar bisa, kamar duniyar da ya kafa har abada.

  3. Ta haka ’ya’yanmu maza a ƙuruciyarsu za su zama kamar tsire-tsiren da aka kula da su, ’ya’yanmu mata kuma za su zama kamar ginshiƙai da sassaƙa don adon fada.

  4. ana iya kama ƙadangare da hannu, duk da haka akan same shi a fadodin sarakuna.

  5. Da a ce ita katanga ce, da sai mu gina hasumiyar azurfa a kanta. Da a ce ita ƙofa ce, da sai mun yi mata ƙyauren itacen al’ul.

  6. Kuraye za su yi ta kuka a kagarorinta, diloli kuma a cikin fadodinta masu alfarma. Lokacinta ya yi kusa, kwanakinta kuma ba za su yi tsawo ba.

  7. Za a ƙyale kagarar, a gudu a bar birnin da dā ake hayaniya; mafaka da hasumiyar tsaro za su zama kango har abada, jin daɗin jakuna, makiyaya don garkuna,

  8. Ƙayayuwa za su mamaye fadodinta ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya za su cika kagaranta. Za tă zama mazaunin diloli da gida don mujiyoyi.

  9. Mutuwa ta haura ta tagoginmu ta kuma shiga katangarmu; ta karkashe ’ya’ya a tituna ta kuma karkashe samari a dandali.

  10. Amma in ba ku yi mini biyayya ba, ba ku kiyaye ranar Asabbaci da tsarki ba, kuka ɗauki wani kaya yayinda kuke shiga ƙofofin Urushalima a ranar Asabbaci, to, sai in cinna wa ƙofofin Urushalima wutar da ba a iya kashewa, tă cinye kagaranta.’ ”

  11. Ya rurrushe kagaransu ya kuma ragargaza biranensu. Ƙasar da dukan waɗanda suke cikinta sun tsorata da jin rurinsa.

  12. Sa’an nan sarkin ya umarci Ashfenaz, shugaban fadarsa yă kawo waɗansu daga cikin Isra’ilawan da suka fito daga gidan sarauta da kuma na fitattun mutane.

  13. Matasa maza waɗanda ba su da wata naƙasa kuma kyawawa, hazikai ta kowace hanyar koyo, sanannu, masu saurin fahimtar abu, da kuma waɗanda suka cancanci su yi aiki a fadar sarki. Zai koya musu harshen Babiloniyawa da kuma littattafansu.

  14. Sarki kuma ya sa a ba su abinci da ruwan inabi kowace rana daga cikin abincin sarki. Za a koyar da su har shekaru uku, bayan haka kuma su shiga yin wa sarki hidima.

  15. Ni, Nebukadnezzar, ina zaune a gidana cikin fadata, ina jin daɗi ina bunkasa.

  16. Sa’an nan sarki ya koma fadarsa ya kwana bai ci ba, kuma babu wata liyafar da aka kawo masa. Ya kuma kāsa barci.

  17. Ku yi shela ga kagarun Ashdod da kuma ga kagarun Masar. “Ku tara kanku a tuddan Samariya; ku ga rashin jituwar da take a cikinta, da kuma zaluncin da ake yi a cikin mutanenta.”

  18. “Ba su ma san yadda za su yi abin da yake daidai ba,” in ji Ubangiji, “sun ɓoye ganima da abubuwan da suka washe a cikin kagarunsu.”

  19. Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “Abokin gāba zai ƙwace ƙasar, zai saukar da mafakarku, zai washe kagarunku.”

  20. Zai kuma zama salamarsu. Sa’ad da Assuriyawa suka kawo wa ƙasarmu hari suka tattake kagarunmu, za mu tā da makiyaya bakwai, har ma shugabannin mutane takwas su yi gāba da su.

  21. Amma Bitrus ya bi daga nesa, har zuwa cikin filin gidan babban firist. Ya shiga, ya zauna tare da masu gadi, don yă ga ƙarshen abin.

  22. In ba haka ba, to, me kuka je kallo? Mutum mai sanye da tufafi masu kyau ne? A’a, masu sa kayan tsada da suke cikin annashuwa, ai, a fada suke.

  23. “Sa’ad da mutum mai ƙarfi, wanda yake da makamai yana gadin gidan kansa, an tsare lafiyar dukiyarsa ke nan.