Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Mountain: Jesus is transfigured upon

27 ayoyi · 11 fannoni

Ayoyi game da Jesus is transfigured upon

Tace bisa littafi
  1. Bayan kwana shida, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, Yaƙub da Yohanna ɗan’uwan Yaƙub, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, su kaɗai.

  2. A can aka sāke kamanninsa a gabansu. Fuskarsa ta haskaka kamar rana, tufafinsa kuwa suka zama fari fat suna walƙiya.

  3. Nan take sai ga Musa da Iliya suka bayyana a gabansu, suna magana da Yesu.

  4. Sai Bitrus ya ce wa Yesu, “Ubangiji, ya yi kyau da muke nan. In kana so, sai in kafa bukkoki uku, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Iliya.”

  5. Yayinda yake cikin magana, sai wani girgije mai haske ya rufe su, sai wata murya daga cikin girgijen ta ce, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna; wanda kuma nake jin daɗinsa ƙwarai. Ku saurare shi!”

  6. Sa’ad da almajiran suka ji haka, sai suka fāɗi ƙasa rubda ciki, a firgice.

  7. Amma Yesu ya zo ya taɓa su ya ce, “Ku tashi, kada ku ji tsoro.”

  8. Da suka ɗaga kai, ba su ga kowa ba sai Yesu kaɗai.

  9. Suna cikin gangarowa daga dutsen ke nan, sai Yesu ya umarce su cewa, “Kada ku faɗa wa kowa abin da kuka gani, sai bayan an tā da Ɗan Mutum daga matattu.”

  10. Bayan kwana shida, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, Yaƙub da Yohanna tare da shi, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, suka kasance su kaɗai a wurin. A can aka sāke kamanninsa a gabansu.

  11. Tufafinsa suka zama fari suna ƙyalli, fiye da yadda wani a duniya zai iya yi su.

  12. Iliya da Musa suka bayyana a gabansu, suna magana da Yesu.

  13. Bitrus ya ce wa Yesu, “Rabbi, ya yi kyau da muke nan. Bari mu kafa bukkoki guda uku, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Iliya.”

  14. (Bai san abin da zai faɗa ba ne, gama sun tsorata ƙwarai.)

  15. Sai wani girgije ya bayyana, ya rufe su, wata murya kuma ta fito daga girgijen, ta ce, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna, ku saurare shi!”

  16. Farat ɗaya, da suka waiwaya, ba su ƙara ganin kowa tare da su ba, sai dai Yesu.

  17. Da suna saukowa daga dutsen, Yesu ya umarce su kada su gaya wa kowa abin da suka gani, sai bayan Ɗan Mutum ya tashi daga matattu.

  18. Suka riƙe wannan zance a ɓoye tsakaninsu, suna tattaunawa ko mece ce ma’anar “tashi daga matattu.”

  19. Bayan kamar kwana takwas da yin wannan magana, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yohanna, da kuma Yaƙub, suka hau kan dutse tare don yin addu’a.

  20. Yana cikin addu’a, sai kamannin fuskarsa ta sāke, tufafinsa kuma suka zama da haske kamar hasken walƙiya.

  21. Sai ga mutum biyu, Musa da Iliya, suka bayyana cikin kyakkyawar daraja, suna magana da Yesu.

  22. Suka yi zance a kan tashinsa, wanda shi ya kusan ya kawo ga cikarsa a Urushalima.

  23. Barci kuwa ya kama Bitrus da abokan tafiyarsa sosai. Da idanunsu suka warware, sai suka ga ɗaukakarsa da kuma mutum biyun tsaye tare da shi.

  24. Da mutanen na barin Yesu, sai Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, ya yi kyau da muke nan. Bari mu kafa bukkoki guda uku, wato, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Iliya.” (Bai ma san abin da yake faɗi ba.)

  25. Yayinda yake cikin magana, sai wani girgije ya bayyana ya rufe su, sai suka ji tsoro, yayinda suke shiga cikin girgijen.