Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Mountain: Removed by faith

3 ayoyi · 11 fannoni

Ayoyi game da Removed by faith

  1. Ya amsa ya ce, “Saboda kuna da ƙarancin bangaskiya sosai. Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiyar da take ƙanƙanuwa kamar ƙwayar mustad, za ku iya ce wa wannan dutse, ‘Matsa daga nan zuwa can,’ zai kuwa matsa. Babu abin da zai gagare ku.”

  2. Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiya, ba kuwa da wata shakka ba, ba kawai za ku iya yin abin da aka yi wa itacen ɓauren nan ba, amma za ku ma iya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka jefa kanka cikin teku,’ sai yă faru.

  3. Gaskiya nake gaya muku, in wani ya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka fāɗa cikin teku,’ bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata cewa, abin da ya faɗa zai faru, haka kuwa za a yi masa.