Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Mountain: Melted

9 ayoyi · 11 fannoni

Ayoyi game da Melted

  1. Sai kuka matso kusa, kuka tsaya a gindin dutse yayinda yana cin wuta har zuwa sararin sama, ga kuma baƙin gizagizai da kuma baƙin duhu.

  2. Sa’ad da kuka ji muryar daga duhu, yayinda dutsen yana cin wuta, dukan manyan kabilanku da dattawanku suka zo wurina.

  3. Duwatsu suka girgizu a gaban Ubangiji, Wannan na Sinai, a gaban Ubangiji, Allah na Isra’ila.

  4. Duwatsu sun narke kamar kakin zuma a gaban Ubangiji, a gaban Ubangijin dukan duniya.

  5. Da ma za ka tsage sammai ka sauko, ai, da duwatsu za su yi rawar jiki a gabanka!

  6. Kamar sa’ad da wuta takan ci rassa ta sa ruwa ya tafasa, ka sauko ka sanar da sunanka ga abokan gābanka ka kuma sa al’ummai su yi rawan jiki a gabanka!

  7. Gama sa’ad da ka aikata abubuwan bantsoron da ba mu sa tsammani ba, ka sauko, duwatsu kuma suka yi rawar jiki a gabanka.

  8. Duwatsu za su narke a ƙarƙashin ƙafafunsa, kamar kaki a gaban wuta, kwaruruka kuma za su ɓace, kamar ruwan da yake gangarowa daga tsauni.

  9. Duwatsu suna rawan jiki a gabansa tuddai kuma sun narke. Duniya da dukan abin da yake cikinta suna rawan jiki a gabansa.