Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Infidelity

97 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Suka ce wa Musa, “Don babu makabarta a Masar ne, ka kawo mu a hamada mu mutu? Me ka yi mana ke nan da ka fitar da mu daga Masar?

  2. Ba mu faɗa maka a Masar ba, cewa ‘Ka bar mu mu bauta wa Masarawa’? Ai, da ya fi mana mu bauta wa Masarawa, da a ce mu mutu a hamada!”

  3. “Har yaushe wannan muguwar al’umma za tă yi gunaguni a kaina? Na ji koke-koken waɗannan Isra’ilawa masu gunaguni.

  4. Saboda haka ka gaya musu cewa, ‘Muddin ina raye, in ji Ubangiji, zan yi muku daidai da abin da na ji kuke faɗa.

  5. A cikin wannan hamadan, jikunanku za su fāɗi, kowanne a cikinku mai shekara ashirin ko fiye, wanda aka ƙirga shi cikin ƙidaya, wanda kuma ya yi gunaguni a kaina, da zai shiga wannan ƙasa.

  6. Ba ko ɗaya daga cikinku da zai shiga ƙasar da na ɗaga hannu na rantse, za tă zama gidanku, sai dai Kaleb ɗan Yefunne da Yoshuwa ɗan Nun.

  7. Amma game da ’ya’yanku da kuka ce za a kwashe ganima, zan kawo su cikin ƙasar, su ji daɗin ƙasar wadda kuka ƙi.

  8. Amma ku, jikunanku za su fāɗi a wannan hamada.

  9. ’Ya’yanku za su zama makiyaya a nan, shekaru arba’in suna shan wahala domin rashin amincinku, har sai mutum na ƙarshe a cikinku ya kwanta a hamada.

  10. Shekaru arba’in, shekara ɗaya a madadi kwana ɗaya cikin kwanakin arba’in da kuka ɗauka kuka leƙi asirin ƙasa, za ku sha wahala saboda zunubanku, ku kuma san abin da ake nufi da sa ni in yi gāba da ku.’

  11. “ ‘Amma duk wanda ya yi zunubi da gangan, ko shi ɗan ƙasa ne, ko baƙo, ya saɓi Ubangiji, dole a ware wannan mutum daga mutanensa,

  12. gama ya rena maganar Ubangiji, ya kuma karya umarninsa. Tabbatacce za a kashe wannan mutum, alhakinsa laifinsa kuwa yana wuyansa.’ ”

  13. Idan kuma wani mutum ya ji kalmomi na wannan rantsuwa, ya kuma sa wa kansa albarka yana tunani cewa, “Ba abin da zai same ni, ko da na nace a taurinkaina.” Wannan zai jawo lalacewar dukan Isra’ila tare da kai.

  14. Ubangiji ba zai gafarce shi ba, fushinsa da kishinsa za su ƙuna a kan wannan mutum. Dukan la’anonin da aka rubuta a wannan littafi za su fāɗo a kansa, Ubangiji kuwa zai shafe sunansa daga ƙarƙashin sama.

  15. Ubangiji zai ware shi daga dukan kabilan Isra’ila don yă hukunta shi bisa ga dukan la’anonin alkawarin da aka rubuta a wannan Littafin Doka.

  16. Daga nan sai Elisha ya tafi Betel. Yayinda yake tafiya a hanya, sai waɗansu matasa suka fito daga cikin gari, suka yi masa dariya suna cewa, “Ka haura, ya kai mai kai marar gashi! Ka haura, kai mai kai marar gashi!”

  17. Sai ya juya ya dube su, ya la’anta su da sunan Ubangiji. Sai beyar guda biyu suka fito daga jeji suka hallaka matasa arba’in da biyu daga cikinsu.

  18. Yanzu fa, kada ku bar Hezekiya yă ruɗe ku yă kuma ɓad da ku haka. Kada ku gaskata shi, gama babu allahn wata ƙasa ko masarautar da ya taɓa iya ceton mutanensa daga hannuna ko kuwa hannun kakannina. Balle har Allahnku yă cece ku daga hannuna!”

  19. Hafsoshin Sennakerib suka ci gaba da maganar banza wa Ubangiji Allah da kuma a kan bawansa Hezekiya.

  20. Sarki ya kuma rubuta wasiƙu yana zagin Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana faɗin wannan a kansa, “Kamar yadda sauran allolin mutanen sauran ƙasashe ba su iya kuɓutar da mutane daga hannuna ba, haka Allahn Hezekiya ba zai kuɓutar da mutanensa daga hannuna ba.”

  21. Sa’an nan suka yi magana da ƙarfi cikin Yahudanci wa mutanen Urushalima waɗanda suke kan katanga, don su firgita su, su kuma sa su ji tsoro don su iya cin birnin.

  22. Suka yi magana game da Allah na Urushalima yadda suka yi game da allolin sauran mutanen duniya, aikin hannuwan mutane.

  23. domin ya nuna wa Allah yatsa ya rena Allah Maɗaukaki,

  24. ya tasar masa da faɗa da garkuwa mai kauri da kuma ƙarfi.

  25. Duk da haka suna ce wa Allah, ‘Ka rabu da mu.’ Ba ma so mu san hanyoyinka.