Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Gospel

110 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Akwai kogi mai rafuffukan da suke sa birnin Allah murna, tsattsarkan wuri inda Mafi Ɗaukaka ke zama.

  2. Allah yana cikinta, ba za tă fāɗi ba; Allah zai taimake ta da safe.

  3. “Lokaci yana zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan yi sabon alkawari da gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda.

  4. Ba zai zama kamar alkawarin da na yi da kakanni kakanninsu ba sa’ad da na kama su da hannu na bishe su daga Masar, domin sun take alkawarina, ko da yake na zama miji a gare su,” in ji Ubangiji.

  5. “Ga alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila bayan wannan lokaci,” in ji Ubangiji. “Zan sa dokata a tunaninsu in kuma rubuta ta a zukatansu. Zan zama Allahnsu, za su kuma zama mutanena.

  6. Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabci ba, ko ya koya wa ɗan’uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji,’ domin duk za su san ni, daga ƙaraminsu har zuwa babba,” in ji Ubangiji. “Gama zan gafarta muguntarsu ba zan kuwa ƙara tuna da zunubansu ba.”

  7. Yesu ya amsa ya ce, “Ku koma ku gaya wa Yohanna abin da kuka ji, kuka kuma gani.

  8. Makafi suna gani, guragu suna tafiya, ana warkar da waɗanda suke da kuturta, kurame suna ji, ana tā da matattu, ana kuma yi wa matalauta wa’azin labari mai daɗi.

  9. Mai albarka ne mutumin da bai yi tuntuɓe ba saboda ni.”

  10. Sai Yesu ya zo wurinsu ya ce, “An ba ni dukan iko a sama da kuma ƙasa.

  11. Saboda haka ku tafi, ku mai da dukan al’umman duniya su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma a cikinsunan Uba, da na Ɗa, da na Ruhu Mai Tsarki,

  12. kuna kuma koya musu, su yi biyayya da duk abin da na umarce ku, kuma tabbatacce, ina tare da ku kullum, har ƙarshen zamani.”

  13. Bayan da aka sa Yohanna a kurkuku, sai Yesu ya shigo cikin Galili, yana shelar bisharar Allah.

  14. Yana cewa, “Lokaci ya yi. Mulkin Allah ya yi kusa. Ku tuba, ku gaskata bishara!”

  15. Mahaifinsa Zakariya ya cika da Ruhu Mai Tsarki sai ya yi annabci ya ce,

  16. “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, domin ya zo ya kuma fanshe mutanensa.

  17. Ya tā mana ƙahon ceto a gidan bawansa Dawuda

  18. (yadda ya yi magana tun tuni ta wurin annabawansa masu tsarki),

  19. cewa zai cece mu daga abokan gābanmu daga kuma hannun dukan waɗanda suke ƙinmu

  20. don yă nuna jinƙai ga kakanninmu, yă kuma tuna da alkawarinsa mai tsarki,

  21. rantsuwar da ya yi wa mahaifinmu Ibrahim,

  22. don yă kuɓutar da mu daga hannun abokan gābanmu, yă kuma sa mu iya yin masa hidima babu tsoro,

  23. cikin tsarki da adalci a gabansa dukan kwanakinmu.

  24. “Kai kuma, ɗana, za a ce da kai annabin Maɗaukaki; gama za ka sha gaban Ubangiji don ka shirya masa hanya,

  25. don ka sanar da mutanensa ceto, ta wurin gafarar zunubansu,