Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Gospel

110 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’ad da Kiristi ya zo a matsayin babban firist na kyawawan abubuwan da suka riga suka kasance a nan, ya bi ta cikin tabanakul mafi girma da kuma mafi cikakke wanda ba mutum ne ya yi ba, wato, ba na wannan halitta ba.

  2. Bai shiga ta wurin jinin awaki da na maruƙa ba; amma ya shiga Wuri Mafi Tsarki sau ɗaya tak ta wurin jininsa, bayan ya samo madawwamiyar fansa.

  3. In har akan yayyafa jinin awaki da na bijimai da kuma tokar karsanar a kan waɗanda suke marasa tsabta bisa ga al’ada, a tsarkake su yadda za su zama masu tsabta a waje,

  4. balle jinin Kiristi, wanda ta wurin Ruhu madawwami ya miƙa kansa marar aibi ga Allah, ai, zai tsabtacce lamirinmu daga ayyukan da suke kai ga mutuwa, don mu bauta wa Allah mai rai!

  5. Saboda haka Kiristi shi ne matsakancin sabon alkawari, don waɗanda aka kira su sami madawwamin gādon da aka yi alkawari, yanzu da ya mutu a matsayin mai fansa don yă ’yantar da su daga zunuban da aka aikata a ƙarƙashin alkawari na farko.

  6. Sai dai kun zo ne ga Dutsen Sihiyona, ga Urushalima ta sama, birnin Allah mai rai. Kun zo ga dubu dubban mala’ikun da suke cikin taron farin ciki,

  7. kun zo ga ikkilisiyar ɗan fari, waɗanda sunayensu suna a rubuce a sama. Kun zo ga Allah, alƙalin dukan mutane, kun kuma zo ga ruhohin mutane masu adalci da aka mai da su cikakku.

  8. Kun zo ga Yesu, mai yin sulhu na sabon alkawari, da kuma ga jinin da aka yayyafa wanda yake magana mafi kyau fiye da jinin Habila.

  9. Sai na ga wani mala’ika yana tashi sama a tsakiyar sararin sama, yana kuma da madawwamiyar bishara wadda zai yi shela ga waɗanda suke zama a duniya, ga kowace al’umma, kabila, harshe, da kuma jama’a.

  10. Ya ce da babbar murya, “Ku ji tsoron Allah ku kuma ɗaukaka shi, domin sa’ar hukuncinsa ya yi. Ku yi wa wannan da ya halicci sammai, ƙasa, teku, da maɓulɓulan ruwa sujada.”