Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Gospel: Called The New Covenant

23 ayoyi · 2 fannoni

Ayoyi game da Called The New Covenant

  1. “Lokaci yana zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan yi sabon alkawari da gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda.

  2. Ba zai zama kamar alkawarin da na yi da kakanni kakanninsu ba sa’ad da na kama su da hannu na bishe su daga Masar, domin sun take alkawarina, ko da yake na zama miji a gare su,” in ji Ubangiji.

  3. “Ga alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila bayan wannan lokaci,” in ji Ubangiji. “Zan sa dokata a tunaninsu in kuma rubuta ta a zukatansu. Zan zama Allahnsu, za su kuma zama mutanena.

  4. Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabci ba, ko ya koya wa ɗan’uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji,’ domin duk za su san ni, daga ƙaraminsu har zuwa babba,” in ji Ubangiji. “Gama zan gafarta muguntarsu ba zan kuwa ƙara tuna da zunubansu ba.”

  5. Amma hidimar da Yesu ya karɓa tana da fifiko a kan tasu, kamar yadda alkawarin da shi ne yake matsakanci ya fi na dā fifiko nesa, an kuma kafa shi a kan alkawura mafi kyau.

  6. Gama da a ce alkawari na fari ba shi da wani laifi, da ba sai an sāke neman wani ba.

  7. Amma Allah ya sami mutane da laifi ya ce, “Ina gaya muku lokaci yana zuwa, sa’ad da zan yi sabon alkawari da gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda.

  8. Ba zai zama kamar irin alkawarin da na yi da kakanni-kakanninsu sa’ad da na kama hannunsu don in fitar da su daga Masar ba, domin ba su yi aminci da alkawarina ba, sai na juya musu baya, in ji Ubangiji.

  9. Wannan shi ne alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila, bayan lokacin nan, in ji Ubangiji. Zan sa dokokina a cikin zukatansu, in kuma rubuta su a kan zukatansu. Zan zama Allahnsu, su kuwa za su zama mutanena.

  10. Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa ba, balle mutum yă ce wa ɗan’uwansa, ‘Ka san Ubangiji,’ domin dukansu za su san ni, daga ƙaraminsu zuwa babba.

  11. Gama zan gafarta muguntarsu ba zan kuma ƙara tuna da zunubansu ba.”

  12. Ta wurin kira wannan alkawari “sabo,” ya mai da na farin tsoho ke nan; abin da yake tsoho yana kuma daɗa tsufa, zai shuɗe nan ba da daɗewa ba.

  13. Ta haka Ruhu Mai Tsarki ya nuna cewa ba a riga an bayyana hanyar shiga Wuri Mafi Tsarki ba tukuna, muddin tabanakul na fari yana nan tsaye.

  14. Wannan ma yana da ma’ana wa mutane a yau. Ya nuna cewa ba za mu iya wanke lamirinmu ta wurin miƙa baye-baye da hadayu ba.

  15. Waɗannan ƙa’idodi sun shafi sha’anin abinci da abin sha ne kawai da kuma ƙa’idodi tsarkake kanmu. Dokoki game da abubuwa na waje da ake amfani da su za su kasance ne sai lokacin ya yi da za a kawo abu mafi kyau.

  16. Sa’ad da Kiristi ya zo a matsayin babban firist na kyawawan abubuwan da suka riga suka kasance a nan, ya bi ta cikin tabanakul mafi girma da kuma mafi cikakke wanda ba mutum ne ya yi ba, wato, ba na wannan halitta ba.

  17. Bai shiga ta wurin jinin awaki da na maruƙa ba; amma ya shiga Wuri Mafi Tsarki sau ɗaya tak ta wurin jininsa, bayan ya samo madawwamiyar fansa.

  18. In har akan yayyafa jinin awaki da na bijimai da kuma tokar karsanar a kan waɗanda suke marasa tsabta bisa ga al’ada, a tsarkake su yadda za su zama masu tsabta a waje,

  19. balle jinin Kiristi, wanda ta wurin Ruhu madawwami ya miƙa kansa marar aibi ga Allah, ai, zai tsabtacce lamirinmu daga ayyukan da suke kai ga mutuwa, don mu bauta wa Allah mai rai!

  20. Saboda haka Kiristi shi ne matsakancin sabon alkawari, don waɗanda aka kira su sami madawwamin gādon da aka yi alkawari, yanzu da ya mutu a matsayin mai fansa don yă ’yantar da su daga zunuban da aka aikata a ƙarƙashin alkawari na farko.

  21. Sai dai kun zo ne ga Dutsen Sihiyona, ga Urushalima ta sama, birnin Allah mai rai. Kun zo ga dubu dubban mala’ikun da suke cikin taron farin ciki,

  22. kun zo ga ikkilisiyar ɗan fari, waɗanda sunayensu suna a rubuce a sama. Kun zo ga Allah, alƙalin dukan mutane, kun kuma zo ga ruhohin mutane masu adalci da aka mai da su cikakku.

  23. Kun zo ga Yesu, mai yin sulhu na sabon alkawari, da kuma ga jinin da aka yayyafa wanda yake magana mafi kyau fiye da jinin Habila.