Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Fasting

31 ayoyi · 41 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. A can, a bakin rafin Ahawa, na sa mu yi azumi, domin mu ƙasƙantar da kanmu a gaban Allah, mu kuma roƙe shi yă kiyaye mana hanya, da mu da ’ya’yanmu da kayanmu duka.

  2. Na ji kunya in roƙi sarki yă haɗa mu da sojoji da masu dawakai don su yi mana rakiya su kāre mu daga magabta a kan hanya, gama mun ce wa sarki, “Alherin Allah yana tare da duk wanda yake dogara gare shi, amma kuma fushinsa yana kan duk wanda ya juya masa baya.”

  3. Saboda haka sai muka yi azumi, muka kai roƙonmu a wurin Allah, ya kuwa amsa mana.

  4. Suna cewa, ‘Don me muka yi azumi, ba ka kuma gani ba? Me ya sa muka ƙasƙantar da kanmu, ba ka kuma lura da wannan ba?’ “Duk da haka a ranar azuminku, kuna yi yadda kuka ga dama kuna kuma zaluntar dukan ma’aikata.

  5. Azuminku yakan ƙare a faɗa da kuma hargitsi, kuna ta naushin juna da mugayen naushe-naushe. Ba za ku iya azumi kamar yadda kuke yi a yau ku zaci za a ji muryarku can sama.

  6. Irin azumin da na zaɓa ke nan, rana guda kawai don mutum ya ƙasƙantar da kansa? Sunkuyar da kanku kamar iwa kawai kuna kuma kwance a tsummoki da toka? Abin da kuke kira azumi ke nan rana yardajje ga Ubangiji?

  7. “Irin azumin da na zaɓa shi ne, a kunce sarƙoƙin rashin adalci a kuma kunce igiyoyin karkiya, a ’yantar da waɗanda ake zalunta a kuma kakkarye kowace karkiya?

  8. Ba shi ne ku rarraba abincinku da mayunwata ku kuma tanada wa matalauta masu yawo mahalli, sa’ad da kuka ga wanda yake tsirara, ku yi masa sutura, kada kuma ku ba wa namanku da jininku baya?

  9. Sa’an nan haskenku zai keto kamar ketowar alfijir, warkarwarku kuma zai bayyana nan da nan; sa’an nan adalcinku zai tafi a gabanku, ɗaukakar Ubangiji kuma zai tsare ku daga baya.

  10. Sa’an nan za ku yi kira, Ubangiji kuma zai amsa; za ku yi kuka don neman taimako, zai kuwa ce ga ni nan. “In kuka kawar da karkiyar zalunci, kuka daina nuna wa juna yatsa da kuma faɗar mugayen maganganu,

  11. in kuma kuka ɗauki lokaci kuka ƙosar da mayunwata kuka kuma biya bukatun waɗanda suke shan tsanani, sa’an nan ne haskenku zai haskaka cikin duhu darenku kuma zai zama kamar tsakar rana.

  12. Ubangiji zai bishe ku kullum; zai biya muku bukatunku a ƙasa mai zafin rana ya kuma ƙarfafa ƙasusuwanku. Za ku zama kamar lambun da aka yi masa banruwa, kamar rafin da ruwansa ba ya ƙafewa.

  13. Mutanenku za su sāke gina kufai na da su kuma daga tsofaffin harsashai; za a ce da ku Masu Gyaran Katangar da ta Rushe, Masu Farfaɗo da Tituna da kuma Wuraren zama.

  14. A wannan lokaci ni Daniyel na yi makoki har na sati uku.

  15. Ban ci abinci mai kyau ba; ba nama ko ruwa inabin da ya shiga bakina; kuma ba na amfani da man shafawa gaba ɗaya har sai da sati nan uku suka wuce.

  16. “Ko yanzu”, in ji Ubangiji, “Ku juyo gare ni da dukan zuciyarku, da azumi da kuka da makoki.”

  17. Ku kyakkece zuciyarku ba rigunanku ba. Ku juyo ga Ubangiji Allahnku, gama shi mai alheri ne mai tausayi kuma mai jinkirin fushi da yawan ƙauna, yakan kuma janye daga aika da bala’i.

  18. Mutanen Ninebe kuwa suka gaskata Allah. Aka yi shela a yi azumi, sai dukansu daga babba har zuwa ƙaraminsu, suka sa tufafin makoki.

  19. Da saƙon Yunana ya kai kunnen sarkin Ninebe, sai ya tashi daga kujerar mulkinsa, ya tuɓe alkyabbarsa, ya sa rigar makoki, ya zauna cikin toka.

  20. Sai ya yi umarni a Ninebe cewa, “Bisa ga umarnin sarki da fadawansa. “Kada a bar wani mutum ko dabba, garke ko shannu, su ɗanɗana wani abu; kada a bari su ci ko su sha.

  21. Bari kowane mutum da dabba yă yafa rigunan makoki. Kowa yă roƙi Allah da gaske, kowa kuma yă bar mugayen ayyukan da yake yi.

  22. “Sa’ad da kuma kuna azumi, kada ku ɓata fuska, yadda munafukai suke yi. Sukan ɓata fuskokinsu domin su nuna wa mutane cewa suna azumi. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun sami ladarsu cikakke.

  23. Amma sa’ad da kana azumi, ka shafa wa kanka mai, ka wanke fuskarka,

  24. domin kada mutane su ga alama cewa kana azumi, sai dai Ubanka kaɗai wanda ba a gani; Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka.

  25. Sai almajiran Yohanna suka zo suka tambaye shi suka ce, “Me ya sa mu da Farisiyawa muke azumi, amma almajiranka ba sa yi?”