Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Fasting

31 ayoyi · 41 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Yesu ya amsa ya ce, “Yaya baƙin ango za su yi makoki yayinda yake tare da su? Lokaci yana zuwa da za a ɗauke ango daga gare su, sa’an nan za su yi azumi.

  2. Suka ce masa, “Almajiran Yohanna sukan yi azumi da addu’a, haka ma almajiran Farisiyawa, amma naka sai ci da sha.”

  3. Yesu ya amsa ya ce, “Za ku iya sa abokan ango yin azumi yayinda yake tare da su?

  4. Amma lokaci yana zuwa, da za a ɗauke ango daga gare su. A waɗancan kwanakin ne za su yi azumi.”

  5. Kafin gari ya waye Bulus ya roƙe su duka su ci abinci. Ya ce, “Kwana goma sha huɗu ke nan, kuna zama cikin zulumi kun kuma kasance ba abinci, ba ku ci kome ba.

  6. Ina roƙonku yanzu ku ci abinci. Kuna bukatarsa don ku rayu. Ba ɗayanku da zai rasa ko gashin kansa guda ɗaya.”