Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Dedication

213 ayoyi · 28 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Gama ka ware su daga dukan al’umman duniya su zama abin gādonka, kamar yadda aka furta ta wurin bawanka Musa sa’ad da kai, ya Ubangiji Mai Iko Duka ka fitar da kakanninmu daga Masar.”

  2. Da Solomon ya gama dukan waɗannan addu’o’i da roƙe-roƙe ga Ubangiji, sai ya tashi daga gaban bagaden Ubangiji, inda ya durƙusa da hannuwansa a buɗe waje sama.

  3. Ya tashi ya kuma albarkaci dukan taron Isra’ila da babbar murya, yana cewa,

  4. “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda ya ba wa mutanensa hutu kamar dai yadda ya yi alkawari. Babu magana guda da ta kāsa cika cikin dukan alkawaransa masu kyau da ya yi ta wurin bawansa Musa.

  5. Bari Ubangiji Allah yă kasance tare da mu kamar yadda ya kasance da kakanninmu; kada yă taɓa rabu da mu, ko yă yashe mu.

  6. Bari yă juye zukatanmu gare shi, don mu yi tafiya a cikin dukan hanyoyinsa, mu kuma kiyaye umarnansa, ƙa’idodinsa, da kuma farillan da ya ba wa kakanninmu.

  7. Bari kuma waɗannan kalmomina, waɗanda na yi addu’a a gaban Ubangiji, su yi kusa da Ubangiji Allahnmu, dare da rana, don yă biya bukatan bawansa da na mutanensa Isra’ila, bisa ga bukatan kowa,

  8. saboda dukan mutanen duniya su san cewa Ubangiji, shi ne Allah, babu kuma wani.

  9. Amma dole ku miƙa zukatanku ga Ubangiji Allahnmu, don ku rayu, ta wurin bin ƙa’idodinsa, ku kuma yi biyayya da umarnansa, kamar yadda kuke yi a wannan lokaci.”

  10. Sai sarki da dukan Isra’ila, suka miƙa hadayu a gaban Ubangiji.

  11. Solomon ya miƙa hadaya ta salama ga Ubangiji, shanu dubu ashirin da biyu, tumaki da awaki dubu ɗari da dubu ashirin. Ta haka sarki da dukan Isra’ilawa suka keɓe haikalin Ubangiji.

  12. Ta haka Solomon ya kiyaye bikin a wannan lokaci har kwana bakwai, dukan Isra’ila kuwa tare da shi, babban taro, mutane daga Lebo Hamat har zuwa Rafin Masar.

  13. A rana ta takwas sai suka yi taro, gama sun yi bikin keɓewar bagade na kwana bakwai da kuma biki na ƙarin kwana bakwai.

  14. A rana ta ashirin da uku na watan bakwai sai ya sallami mutane su tafi gidajensu da farin ciki da kuma murna a zuciya saboda abubuwa masu kyau da Ubangiji ya yi domin Dawuda da Solomon da kuma domin mutanensa Isra’ila.

  15. Sai mutanen Isra’ila, firistoci, Lawiyawa da kuma sauran waɗanda suka dawo daga bauta suka yi bikin keɓe gidan Allah, cike da farin ciki.

  16. Suka miƙa bijimai guda ɗari, da raguna ɗari biyu, da ’yan raguna ɗari huɗu. Suka kuma miƙa hadayu don zunubi saboda dukan Isra’ila, suka kuma miƙa bunsurai guda goma sha biyu don hadaya ta zunubi, kowane bunsuru ɗaya don kowace kabila ta Isra’ila.

  17. A keɓewar katangar Urushalima, an nemi Lawiyawa daga inda suke zama aka kawo su Urushalima don su yi bikin miƙawa da farin ciki da waƙoƙin godiya da kuma kiɗin kuge, garaya da molo.

  18. Aka kuma tattara mawaƙa su ma daga yankin kewayen Urushalima, daga ƙauyukan Netofawa,

  19. daga Bet-Gilgal, da kuma daga wuraren Geba da Azmawet, gama mawaƙan sun gina wa kansu ƙauyuka kewaye da Urushalima.

  20. Sa’ad da firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu da tsarki, sai suka tsarkake mutane, ƙofofi da kuma katanga.

  21. Sai na sa shugabannin Yahuda suka haura zuwa bisan katangar. Na kuma sa manyan ƙungiyoyi biyu na mawaƙa su miƙa godiya. Ɗaya ya haura zuwa bisan katangar zuwa dama, wajen Ƙofar Juji.

  22. Hoshahiya da rabin shugabannin Yahuda kuwa suka bi su,

  23. tare da Azariya, Ezra, Meshullam,

  24. Yahuda, Benyamin, Shemahiya, Irmiya,

  25. da waɗansu firistoci kuma da ƙahoni, da kuma Zakariya ɗan Yonatan, ɗan Shemahiya, ɗan Mattaniya, ɗan Mikahiya, ɗan Zakkur, ɗan Asaf,