Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Ablution

52 ayoyi · 10 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Mutumin da yake da tsarki, zai tara tokar karsanar, yă sa ta a wurin da yake da tsabta a bayan sansani. Jama’ar Isra’ilawa ne za su adana shi don amfani a ruwan tsabtaccewa; wannan domin tsarkakewa ne daga zunubi.

  2. Dole mutumin da ya tara tokar karsanar yă wanke rigunarsa, zai kuwa kasance da ƙazanta har yamma. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ta har abada ga Isra’ilawa, da kuma baƙin da suke zama a cikinsu.

  3. A rana ta uku, da ta bakwai kuma mai tsarkakewa zai yayyafa wa marar tsarkin ruwa, a rana ta bakwai kuma yă tsarkake shi. Wanda aka tsarkaken kuwa, dole yă wanke rigunarsa, yă kuma yi wanka da yamma, zai kuma tsarkaka.

  4. Sa’an nan dukan dattawan garin da yake kurkusa da gawar za su wanke hannuwansu a bisa karsanan da aka karye wuyar a kwarin,

  5. Saboda haka sai kai shi zuwa gidansa ya ciyar da jakunansa. Bayan sun wanke ƙafafunsu, sai aka ba su abinci da abin sha.

  6. Sa’an nan Dawuda ya ce wa Uriya, “Gangara gidanka ka wanke ƙafafunka.” Saboda haka Uriya ya bar fadar, sarki kuma ya aika masa da kyauta.

  7. Sa’an nan ya yi daruna goma don wanki ya sa biyar a gefen kudu, biyar kuma a gefen arewa. A cikinsu kayan da za a yi amfani don ɗauraye hadayun ƙonawa, amma firistoci suna amfani da ƙaton kwano mai suna Teku don wanki.

  8. Na wanke hannuwana cikin rashin laifi, ina yawo a bagadenka Ya Ubangiji,

  9. Na tuɓe rigata, sai in sāke sa ta kuma? Na wanke ƙafafuna, sai in sāke ɓata su?

  10. A ranar da aka haife ki ba a yanke cibiyarki ba, ba a kuma yi miki wanka don a tsabtacce ki ba, ba a kuma goge ki da gishiri ba ko a naɗe ki cikin tsummoki.

  11. Amma sa’ad da kana azumi, ka shafa wa kanka mai, ka wanke fuskarka,

  12. “Me ya sa almajiranka suke karya al’adun dattawa? Ba sa wanke hannuwansu kafin su ci abinci!”

  13. Da Bilatus ya ga cewa ba ya kaiwa ko’ina, sai ma hargitsi ne yake so yă tashi, sai ya ɗibi ruwa, ya wanke hannuwansa a gaban taron ya ce, “Ni kam, ba ruwana da alhakin jinin mutumin nan. Wannan ruwanku ne!”

  14. Sai suka ga waɗansu daga cikin almajiransa suna cin abinci da hannuwa marasa tsabta, wato, da ba a wanke ba.

  15. (Farisiyawa da dukan Yahudawa ba sa cin abinci, sai sun wanke hannuwa sarai tukuna, yadda al’adun dattawa suka ce.

  16. Sa’ad da suka dawo daga wurin kasuwanci, dole su wanke hannu kafin su ci abinci. Sukan kuma kiyaye waɗansu al’adu da yawa, kamar wanken kwafuna, tuluna da butoci.)

  17. Saboda haka, Farisiyawa da malaman dokoki suka tambayi Yesu, suka ce, “Don me almajiranka ba sa bin al’adun dattawa, a maimakon haka suna cin abinci da hannuwa marasa tsabta?”

  18. Kun yar da umarnan Allah, kuna bin al’adun mutane.”

  19. Ya kuma ce musu, “Kuna da hanya mai sauƙi na ajiye umarnan Allah a gefe ɗaya, don ku kiyaye al’adunku!

  20. ta kuma tsaya daga bayansa, wajen ƙafafunsa tana kuka, sai hawayenta sun fara zuba a ƙafafunsa. Sai ta goge su da gashin kanta, ta sumbace su, sa’an nan ta shafa musu turare.

  21. Sai ya juya wajen macen, ya ce wa Siman, “Ka ga macen nan? Na shigo gidanka, ba ka ba ni ruwa don ƙafafuna ba, amma ta wanke ƙafafuna da hawayenta, ta kuma goge su da gashin kanta.

  22. Amma Bafarisiyen ya lura cewa, Yesu bai wanke hannu kafin ya ci abinci ba, sai mamaki ya kama shi.

  23. Sai Ubangiji ya ce masa, “Ku Farisiyawa, kukan wanke bayan kwano da kwaf, amma a ciki kuna cike da kwaɗayi da mugunta.

  24. Bayan haka, sai ya zuba ruwa a cikin kwano, sa’an nan ya fara wanke ƙafafun almajiransa, yana sharewa da tawul wanda ya ɗaura.

  25. A lokacin nan ta yi rashin lafiya ta mutu, aka kuma yi wa gawarta wanka aka ajiye a wani ɗaki a gidan sama.