Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Luka 4:7kusan 27 M.

    Saboda haka in ka yi mini sujada, dukan wannan zai zama naka.”

  2. Luka 4:8kusan 27 M.

    Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta wa.’”

  3. Luka 4:9kusan 27 M.

    Sai Iblis, ya kai shi Urushalima ya sa ya tsaya a kan wuri mafi tsayi na haikali ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka yi tsalle daga nan zuwa ƙasa.

  4. Luka 4:10kusan 27 M.

    Gama a rubuce yake, “ ‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai, su kiyaye ka da kyau;

  5. Luka 4:11kusan 27 M.

    za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’”

  6. Luka 4:12kusan 27 M.

    Yesu ya amsa ya ce, “An ce, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’”

  7. Luka 4:13kusan 27 M.

    Da Iblis ya gama dukan wannan gwajin, ya bar shi sai lokacin da wata dama ta samu.

  8. Luka 4:14kusan 27 M.

    Yesu ya koma Galili cikin ikon Ruhu. Labarinsa kuwa ya bazu ko’ina a ƙauyuka.

  9. Luka 4:15kusan 27 M.

    Ya yi ta koyarwa a majami’unsu, kowa kuwa ya yabe shi.

  10. Luka 4:16kusan 27 M.

    Ya tafi Nazaret, inda aka yi renonsa. A ranar Asabbaci kuma, ya shiga majami’a kamar yadda ya saba. Sai ya miƙe don yă yi karatu.

  11. Luka 4:17kusan 27 M.

    Aka kuwa ba shi naɗaɗɗen littafin annabi Ishaya. Da ya buɗe, sai ya sami wurin da aka rubuta,

  12. Luka 4:18kusan 27 M.

    “Ruhun Ubangiji yana kaina, domin ya shafe ni, in yi wa matalauta wa’azin bishara. Ya aiko ni in yi shelar ’yanci ga ’yan kurkuku, in kuma buɗe idanun makafi, in ba da ’yanci ga waɗanda aka danne.

  13. Luka 4:19kusan 27 M.

    In yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji.”

  14. Luka 4:20kusan 27 M.

    Sai ya naɗe naɗaɗɗen littafin ya mayar wa mai hidimar, ya kuma zauna. Dukan idanun waɗanda suke a majami’ar, suka koma a kansa.

  15. Luka 4:21kusan 27 M.

    Sai ya fara ce musu, “A yau, Nassin nan, ya cika a kunnenku.”

  16. Luka 4:22kusan 27 M.

    Duk suka yabe shi, suka yi mamakin kalmomin alheri da suke fitowa daga bakinsa. Suka yi tambaya, suna cewa, “Anya, wannan ba ɗan Yusuf ba ne?”

  17. Luka 4:23kusan 27 M.

    Yesu ya ce musu, “Tabbatacce, na san za ku faɗa mini karin maganan nan, ‘Likita, warkar da kanka! Ka kuma yi abin da muka ji ka yi a Kafarnahum, a nan garinka.’ ”

  18. Luka 4:24kusan 27 M.

    Ya ci gaba, da ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, babu annabin da ake yarda da shi a garinsa.

  19. Luka 4:25kusan 27 M.

    Ina tabbatar muku a zamanin Iliya, akwai gwauraye da yawa a Isra’ila, sa’ad da aka rufe sararin sama har shekara uku da rabi, aka kuma yi yunwa mai tsanani ko’ina a ƙasar.

  20. Luka 4:26kusan 27 M.

    Duk da haka, ba a aiki Iliya ga ko ɗaya a cikinsu ba. Sai dai zuwa ga wata gwauruwa da take a Zarefat, a yankin Sidon.

  21. Luka 4:27kusan 27 M.

    Akwai kuma mutane da yawa a Isra’ila masu kuturta a zamanin annabi Elisha, amma ba ko ɗayansu da aka tsarkake sai Na’aman mutumin Suriyan nan kaɗai.”

  22. Luka 4:28kusan 27 M.

    Dukan mutanen da suke cikin majami’a suka fusata ƙwarai da jin wannan.

  23. Luka 4:29kusan 27 M.

    Suka tashi, suka fitar da Yesu bayan gari, suka kai shi goshin tudun da aka gina garin, don su ture shi ƙasa,

  24. Luka 4:30kusan 27 M.

    amma sai ya bi ta tsakiyar taron ya yi tafiyarsa.

  25. Luka 4:31kusan 27 M.

    Sai ya tafi Kafarnahum, wani gari a Galili, a ranar Asabbaci kuma, ya fara koya wa mutane.