circa 800–400 BC
The Hebrew Prophets
God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ishaya 62:1kusan 698 K.H.
Saboda Sihiyona ba zan yi shiru ba, saboda Urushalima ba zan huta ba, sai adalcinta ya haskaka kamar hasken safiya, cetonta kuma ya haskaka kamar fitila mai haske.
- Ishaya 62:2kusan 698 K.H.
Al’ummai za su ga adalcinki, sarakuna kuma za su ga ɗaukakarki; za a kira ki da sabon suna sunan da bakin Ubangiji zai ambata.
- Ishaya 62:3kusan 698 K.H.
Za ki zama rawanin daraja a hannun Ubangiji, rawanin sarauta a hannun Allahnki.
- Ishaya 62:4kusan 698 K.H.
Ba za a ƙara ce da ke Yasasshiya ba, ko a kira ƙasarki Kango. Amma za a ce da ke Hefziba ƙasarki kuma Bewula; gama Ubangiji zai ji daɗinki, ƙasarki kuma za tă yi aure.
- Ishaya 62:5kusan 698 K.H.
Kamar yadda saurayi kan auri yarinya, haka ’ya’yanki maza za su aure ki; kamar kuma yadda ango yakan yi farin ciki da amaryarsa, haka Allahnki zai yi farin ciki da ke.
- Ishaya 62:6kusan 698 K.H.
Na sa matsara a kan katangarki, ya Urushalima; ba za su taɓa yin shiru ba, dare da rana. Ku da kuke kira bisa sunan Ubangiji, kada ku ba kanku hutu,
- Ishaya 62:7kusan 698 K.H.
kuma kada ku ba shi hutu sai ya kafa Urushalima ya kuma mai da ita yabon duniya.
- Ishaya 62:8kusan 698 K.H.
Ubangiji ya rantse da hannunsa na dama ta hannunsa kuma mai iko cewa, “Ba zan ƙara ba da hatsinki ya zama abinci ga abokan gābanki ba, baƙi kuma ba za su ƙara shan ruwan inabin wanda kika sha wahala samu ba;
- Ishaya 62:9kusan 698 K.H.
amma waɗanda suka girbe shi za su ci shi su kuma yabi Ubangiji, waɗanda kuma suka tattara ’ya’yan inabi za su sha shi a filayen wurina mai tsarki.”
- Ishaya 62:10kusan 698 K.H.
Ku wuce, ku wuce ƙofofi! Ku shirya hanya saboda mutane. Ku gina, ku gina babbar hanya! Ku kawar da duwatsu. Ku ɗaga tuta saboda al’ummai.
- Ishaya 62:11kusan 698 K.H.
Ubangiji ya yi shela ga iyakokin duniya cewa, “Faɗa wa Diyar Sihiyona, ‘Ga Mai Cetonki yana zuwa! Ga ladarsa tana tare da shi, sakamakonsa yana raka shi.’ ”
- Ishaya 62:12kusan 698 K.H.
Za a ce da shi Tsattsarkar Mutane, Fansassu na Ubangiji; za a kuma ce da ke Wadda Aka Nema Birnin da Ba Za a Ƙara Yashe ta ba.
- Ishaya 63:1kusan 698 K.H.
Wane ne wannan mai zuwa daga Edom, daga Bozra, saye da jajjayen rigunarsa? Wane ne wannan, sanye cikin daraja, tafe cikin girmar ƙarfinsa? “Ni ne, mai magana cikin adalci, mai ikon ceto.”
- Ishaya 63:2kusan 698 K.H.
Me ya sa rigunanka suka yi ja, sai ka ce na wanda yake tattaka ’ya’yan inabi?
- Ishaya 63:3kusan 698 K.H.
“Na tattake ’ya’yan inabi ni kaɗai; cikin al’ummai kuma babu wani tare da ni. Na tattake su cikin fushina Na matse su cikin hasalata; jininsu ya fantsamar wa rigunana, na kuma ɓata dukan tufafina.
- Ishaya 63:4kusan 698 K.H.
Gama ranar ɗaukan fansa tana a cikin zuciyata, kuma shekarar fansata ta zo.
- Ishaya 63:5kusan 698 K.H.
Na duba, amma babu wanda zai taimaka, na yi mamaki cewa ba wanda ya goyi baya; saboda haka hannuna ya yi mini ceto, fushina kuma ya rayar da ni.
- Ishaya 63:6kusan 698 K.H.
Na tattake al’ummai cikin fushina; cikin hasalata kuma na sa sun bugu na kuma zub da jininsu a ƙasa.”
- Ishaya 63:7kusan 698 K.H.
Zan ba da labarin alherin Ubangiji, ayyukan da suka sa a yabe shi, bisa ga dukan abubuwan da Ubangiji ya yi mana, I, ayyuka masu kyan da ya yi domin gidan Isra’ila, bisa ga jinƙansa da yawan alheransa.
- Ishaya 63:8kusan 698 K.H.
Ya ce, “Babu shakka su mutanena ne, ’ya’ya maza waɗanda ba za su ruɗe ni ba”; ta haka ya zama Mai Cetonsu.
- Ishaya 63:9kusan 698 K.H.
Cikin dukan damuwarsu shi ma ya damu, mala’ikan da yake gabansa ya cece su. Cikin ƙauna da jinƙai ya fanshe su; ya kuma ɗaga su ya riƙe su dukan kwanakin dā
- Ishaya 63:10kusan 698 K.H.
Duk da haka suka yi tawaye suka ɓata wa Ruhu Mai Tsarki rai. Saboda haka ya juya ya kuma zama abokin gābansu shi kansa kuma ya yaƙe su.
- Ishaya 63:11kusan 698 K.H.
Sa’an nan mutanensa suka tuna kwanakin dā, kwanakin Musa da mutanensa, ina yake shi wanda ya fitar da su ta teku, da makiyayan garkensa? Ina shi yake wanda ya sa Ruhunsa Mai Tsarki a cikinsu,
- Ishaya 63:12kusan 698 K.H.
wanda ya aika hannu ɗaukakarsa mai iko ya kasance a hannun dama na Musa, wanda ya raba ruwaye a gabansu, don yă sami wa kansa madawwamin suna,
- Ishaya 63:13kusan 698 K.H.
wanda ya bishe su cikin zurfafa? Kamar doki a fili, ba su yi tuntuɓe ba;