Tsallake zuwa abun ciki

circa 605–538 BC

The Babylonian Exile

Jerusalem falls and the temple burns; Ezekiel and Daniel minister among the exiles as Lamentations mourns the city's ruin.

1,784 ayoyi · 3 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Za su zama kango a cikin ƙasashen da suke kango, biranensu kuwa za su zama kufai a cikin biranen da suka lalace.

  2. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da suka ga na sa wuta wa Masar aka kuma ragargaza masu taimakonta.

  3. “ ‘A wannan rana manzanni za su fito daga wurina a jiragen ruwa don su tsorata Kush daga sake jikinta. Azaba za tă kama su a ranar hallakar Masar, gama tabbatacce za tă zo.

  4. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Zan kawo ƙarshen mutanen Masar ta hannun Nebukadnezzar sarkin Babilon.

  5. Shi da sojojinsa, mafi bantsoro cikin al’ummai, za a kawo don su hallaka ƙasar. Za su zāre takuba a kan Masar su kuma cika ƙasar da kisassu.

  6. Zan kafe rafuffukan Nilu in sayar da ƙasar ga mugayen mutane; ta hannun baƙi zan sa ƙasar ta lalace da kome da yake cikinta. Ni Ubangiji na faɗa.

  7. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Zan hallaka gumaka in kuma kawo ƙarshen siffofi a Memfis. Ba za a ƙara samun yerima a ƙasar Masar ba, zan kuma baza tsoro a duk fāɗin ƙasar.

  8. Zan lalace Masar ta Bisa in ƙuna wuta wa Zowan in zartar da hukunci a kan Tebes.

  9. Zan kwarara hasalata a kan Felusiyum, kagarar Masar, in kuma datse mutanen Tebes.

  10. Zan ƙuna wuta wa Masar; Felusiyum za tă sha azaba mai zafi. Za a tayar wa Tebes da hankali; Memfis za tă riƙa kasance cikin ɓacin rai.

  11. Samarin Heliyofolis da Bubastis za su mutu ta wurin takobi, biranen kansu za su tafi bauta.

  12. Duhu ne zai zama rana a Tafanes sa’ad da na karye ikon Masar; a can ƙarfin da take fariya zai ƙare. Za a rufe ta da gizagizai ƙauyukanta kuma za su tafi bauta.

  13. Ta haka zan zartar da hukunci a kan Masar, za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji.’ ”

  14. Ezekiyel 30:20kusan 588 K.H.

    A shekara ta goma sha ɗaya, a wata na fari a rana ta goma sha bakwai, maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

  15. Ezekiyel 30:21kusan 588 K.H.

    “Ɗan mutum, na karye hannun Fir’auna sarkin Masar. Ba a daure shi don warkarwa ba ko a sa tsinke saboda kada yă zama da ƙarfi har ya riƙe takobi.

  16. Ezekiyel 30:22kusan 588 K.H.

    Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da Fir’auna sarkin Masar. Zan karye hannuwansa biyu, hannun da yake da kyau da kuma wanda an riga an karya, in kuma sa takobi ya fāɗi daga hannunsa.

  17. Ezekiyel 30:23kusan 588 K.H.

    Zan watsar da Masarawa a cikin al’ummai in warwatsa su cikin ƙasashe.

  18. Ezekiyel 30:24kusan 588 K.H.

    Zan ƙarfafa hannuwan sarkin Babilon in kuma sa takobina a hannunsa, amma zan karya hannuwan Fir’auna, zai kuwa yi nishi a gabansa kamar mutumin da aka yi wa raunin mutuwa.

  19. Ezekiyel 30:25kusan 588 K.H.

    Zan ƙarfafa hannuwan sarkin Babilon, amma hannuwan Fir’auna za su shanye. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na sa takobi a hannun sarkin Babilon na kuma miƙa shi a kan Masar.

  20. Ezekiyel 30:26kusan 588 K.H.

    Zan watsar da Masarawa a cikin al’ummai in warwatsa su cikin ƙasashe. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.”

  21. Ezekiyel 31:1kusan 588 K.H.

    A shekara ta goma sha ɗaya, a wata na uku a rana ta farko, maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

  22. Ezekiyel 31:2kusan 588 K.H.

    “Ɗan mutum, faɗa wa Fir’auna sarkin Masar da jama’arsa cewa, “ ‘Da wa za a kwatanta girmanka?

  23. Ezekiyel 31:3kusan 588 K.H.

    Ka dubi Assuriya, ta taɓa zama kamar al’ul a Lebanon da rassa masu kyau suna inuwartar da kurmi; ya yi tsayi ainun kansa ya kai cikin gizagizai.

  24. Ezekiyel 31:4kusan 588 K.H.

    Ruwa ya sa ya yi girma, zurfafan maɓulɓulai sun sa ya yi tsayi; rafuffuka suna gudu kewaye da tushensa yana aika da rafuffukansa zuwa dukan itatuwan kurmi.

  25. Ezekiyel 31:5kusan 588 K.H.

    Saboda haka ya yi tsayi fiye da sauran itatuwan kurmi; rassansa suka ƙaru suka yi tsayi, suka bazu saboda yalwar ruwaye.