Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Sinai & The Law

God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.

1,657 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Firistoci 15:5kusan 1490 K.H.

    Duk wanda ya taɓa gadonsa dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuwa ƙazantu har yamma.

  2. Firistoci 15:6kusan 1490 K.H.

    Duk wanda ya zauna a inda wannan mai ɗiga ya zauna a kai, dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuwa ƙazantu har yamma.

  3. Firistoci 15:7kusan 1490 K.H.

    “ ‘Duk wanda ya taɓa jikin mai ɗiga, dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.

  4. Firistoci 15:8kusan 1490 K.H.

    “ ‘In mai ɗiga ya tofa miyau a kan wani wanda yake tsarkakakke, dole tsarkakakken nan yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.

  5. Firistoci 15:9kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kowane sirdi da mai ɗigar ya zauna a kai zai ƙazantu,

  6. Firistoci 15:10kusan 1490 K.H.

    kuma duk wanda ya taɓa wani abu cikin abubuwan da suke a ƙarƙashin sirdin zai ƙazantu har yamma; duk wanda ya ɗauki abubuwan nan dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuwa ƙazantu har yamma.

  7. Firistoci 15:11kusan 1490 K.H.

    “ ‘Duk wanda mai ɗiga ya taɓa ba tare da ya wanke hannuwansa da ruwa ba, dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.

  8. Firistoci 15:12kusan 1490 K.H.

    “ ‘Dole a farfashe tukunya lakar da mutumin ya taɓa, kuma dole a ɗauraye duk wani abin da aka yi da katako wanda ya taɓa da ruwa.

  9. Firistoci 15:13kusan 1490 K.H.

    “ ‘Sa’ad da aka tsabtacce mai ɗigar, zai ɗauki kwana bakwai don tsabtaccewarsa; dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka mai tsabta, zai kuwa zama tsarkakakke.

  10. Firistoci 15:14kusan 1490 K.H.

    A rana ta takwas dole yă ɗauki kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu, yă zo gaban Ubangiji a ƙofar Tentin Sujada, yă ba da su ga firist.

  11. Firistoci 15:15kusan 1490 K.H.

    Firist ɗin zai miƙa su, ɗaya domin hadaya don zunubi, ɗayan kuma domin hadaya ta ƙonawa. Ta haka zai yi kafara a gaban Ubangiji saboda mai ɗigar.

  12. Firistoci 15:16kusan 1490 K.H.

    “ ‘Sa’ad da namiji ya ɗigar maniyyi, dole yă wanke jikinsa gaba ɗaya da ruwa, zai kuma ƙazantu har yamma.

  13. Firistoci 15:17kusan 1490 K.H.

    Dole a wanke duk riga ko fatar da yake da maniyyin a kansa da ruwa, zai kuma ƙazantu har yamma.

  14. Firistoci 15:18kusan 1490 K.H.

    Sa’ad da namiji ya kwana da mace ya kuwa zub da maniyyi, dole dukansu biyu su yi wanka, za su kuma ƙazantu har yamma.

  15. Firistoci 15:19kusan 1490 K.H.

    “ ‘Sa’ad mace take al’adarta ta ƙa’ida, rashin tsabtarta ta al’adar zai ɗauki kwana bakwai, kuma duk wanda ya taɓa ta, zai ƙazantu har yamma.

  16. Firistoci 15:20kusan 1490 K.H.

    “ ‘Duk abin da ta kwanta a kai a lokacin al’adarta zai ƙazantu, kuma duk abin da ta zauna a kai zai ƙazantu.

  17. Firistoci 15:21kusan 1490 K.H.

    Duk wanda ya taɓa gadonta dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.

  18. Firistoci 15:22kusan 1490 K.H.

    Duk wanda ya taɓa wani abin da ta zauna a kai, dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.

  19. Firistoci 15:23kusan 1490 K.H.

    Ko gado ne, ko kuwa wani abin da ta zauna a kai, sa’ad da wani ya taɓa shi, zai ƙazantu har yamma.

  20. Firistoci 15:24kusan 1490 K.H.

    “ ‘In namiji ya kwana da ita, al’adarta kuwa ta taɓa shi, zai ƙazantu na kwana bakwai; duk kuma gadon da ya kwanta a kai, zai ƙazantu.

  21. Firistoci 15:25kusan 1490 K.H.

    “ ‘Idan mace tana ɗigar jini na tsawon kwanaki, ban da kwanakin ganin al’adarta, ko kuwa idan al’adarta ya wuce yawan kwanakin da ya kamata, to, za tă ƙazantu daidai kamar na kwanakin al’adar da ta saba yi. Wato, muddin tana cikin ɗiga, ta zama mai ƙazanta.

  22. Firistoci 15:26kusan 1490 K.H.

    Duk gadon da ta kwanta yayinda ta ci gaba da ɗiga zai zama marar tsarki, kamar yadda gadonta yake a lokacin al’adarta, kuma duk abin da ta zauna a kai zai zama marar tsarki, kamar yadda yake a lokacin al’adarta.

  23. Firistoci 15:27kusan 1490 K.H.

    Duk wanda ta taɓa su zai zama marar tsarki; dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.

  24. Firistoci 15:28kusan 1490 K.H.

    “ ‘Sa’ad da aka tsabtacce ta daga ɗigarta, dole tă ɗauki kwana bakwai, bayan haka za tă zama mai tsarki.

  25. Firistoci 15:29kusan 1490 K.H.

    A rana ta takwas, dole tă ɗauki kurciyoyi biyu ko tattabari biyu ta kawo su ga firist a bakin ƙofar Tentin Sujada.