Tsallake zuwa abun ciki

Moses

774 ayoyi · 7 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Moses

Tace bisa littafi
  1. Amma Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna. “Tun da yake ba ku gaskata ni ba, ba ku kuwa ɗaukaka ni a idon Isra’ilawa ba, to, ba za ku kai taron jama’an nan a ƙasar da na ba su ba.”

  2. Musa ya aiki manzanni daga Kadesh zuwa wurin sarkin Edom cewa, “Ga abin da ɗan’uwanka Isra’ila ya ce ka san duk irin wahalolin da ya same mu.

  3. A Dutsen Hor, kusa da iyakar Edom, Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,

  4. Musa ya yi yadda Ubangiji ya umarta. Suka hau Dutsen Hor a idon dukan jama’a.

  5. Musa ya tuɓe taguwar Haruna, ya kuma sa wa Eleyazar ɗan Haruna. Nan kuwa Haruna ya mutu a bisa dutsen. Sa’an nan Musa da Eleyazar suka sauka daga dutsen,

  6. suka yi wa Allah da Musa gunaguni, suka ce, “Me ya sa kuka fitar da mu daga Masar, kuka kawo mu mu mutu a wannan hamada? Babu abinci! Babu ruwa! Mu dai mun gaji da wannan abinci marar amfani!”

  7. Mutanen suka zo wurin Musa, suka ce, “Mun yi zunubi, da muka yi wa Ubangiji da kai gunaguni. Ka yi addu’a don Ubangiji yă ɗauke mana macizan nan.” Saboda haka Musa ya yi addu’a domin mutane.

  8. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ƙera siffar maciji ka rataye shi a bisa doguwar sanda; kowa da maciji ya sare shi, idan ya dubi macijin nan da ka rataye, zai rayu.”

  9. Saboda haka Musa ya ƙera macijin tagulla, ya kuma rataye shi bisa doguwar sanda. Sa’an nan duk wanda maciji ya sare shi, ya kuma dubi macijin tagullar, zai warke.

  10. Daga can, suka gangara zuwa Beyer, wato, rijiyar da Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka tattara mutane duka, zan kuwa ba su ruwa.”

  11. Sai Musa ya aika ’yan leƙen asiri zuwa Yazer. Daga baya, sai Isra’ilawa suka ci ƙauyukan da suke kewaye, suka kuma kori Amoriyawa da suke zaune a can.

  12. Ubangiji ya ce wa Musa, “Kada ka ji tsoronsa, gama na ba da shi a gare ka, da dukan sojojinsa da kuma ƙasarsa. Ka yi da shi yadda ka yi da Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon.”

  13. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka kama dukan shugabannin mutanen nan, ka kashe su, ka kuma bar su a tsakar rana a gaban Ubangiji, don Ubangiji yă huce daga fushin da nake yi da Isra’ila.”

  14. Saboda haka Musa ya ce wa alƙalan Isra’ila, “Dole kowannenku yă kashe mutanen nan da suka haɗa kai cikin bautar Ba’al-Feyor.”

  15. Sa’an nan wani mutumin Isra’ila ya kawo wata Bamidiyana a iyalinsa a idon Musa da dukan taron jama’ar Isra’ila, yayinda suke kuka a ƙofar Tentin Sujada.

  16. Ubangiji ya ce wa Musa,

  17. Ubangiji ya ce wa Musa,

  18. Bayan annobar, sai Ubangiji ya yi magana da Musa da Eleyazar ɗan Haruna, firist ya ce,

  19. Musa da Eleyazar firist suka yi musu magana a filayen Mowab kusa da Urdun daga ƙetaren Yeriko, suka ce,

  20. “Ku ƙidaya maza daga mai shekara ashirin zuwa gaba yadda Ubangiji ya umarci Musa.” Waɗannan su ne Isra’ilawan da suka fito daga Masar.

  21. ’ya’yan Eliyab maza kuwa su ne, Nemuwel, Datan da Abiram. Datan da Abiram nan, su ne shugabannin mutanen da suka tayar wa Musa da Haruna, suna kuma cikin waɗanda suka bi Kora sa’ad da ya tayar wa Ubangiji.

  22. Ubangiji ya ce wa Musa,

  23. sunan matan Amram shi ne Yokebed, ita zuriyar Lawi ce, wadda aka haifa wa Lawiyawa a Masar. A wajen Amram kuwa ta haifi Haruna, Musa da kuma ’yar’uwarsu Miriyam.

  24. Waɗannan su ne waɗanda Musa da Eleyazar firist, suka ƙidaya sa’ad da suka ƙidaya Isra’ilawa a filaye Mowab kusa da Urdun a hayen Yeriko.

  25. Ba ko ɗayansu da yake cikin waɗanda Musa da Haruna firist, suka ƙidaya sa’ad da suka ƙidaya Isra’ilawa a Hamadar Sinai.