Tsallake zuwa abun ciki

Moab

151 ayoyi · 5 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Moab

Tace bisa littafi
  1. A wannan rana aka mai da Mowab bayin Isra’ila, ƙasar kuwa ta sami zaman lafiya shekara takwas.

  2. Isra’ilawa suka sāke yin mugayen ayyuka a gaban Ubangiji. Suka shiga bautar Ba’al da Ashtarot, da kuma allolin Aram, allolin Sidon, allolin Mowab, Ammonawa da kuma allolin Filistiyawa. Kuma domin Isra’ilawa sun bar Ubangiji ba su ƙara bauta masa ba,

  3. yana cewa, “Ga abin da Yefta yake faɗi, Isra’ila ba tă ƙwace ƙasar Mowab ko ta Ammonawa ba.

  4. Sa’an nan Isra’ila ta aiki jakadu zuwa ga sarkin Edom cewa, ‘Ka ba mu izini mu ratsa ƙasarka,’ amma sarkin Edom bai saurara ba. Suka kuma aika wa sarkin Mowab, shi ma ya ƙi. Saboda haka Isra’ila ta zauna a Kadesh.

  5. “Daga can suka ci gaba ta hamada, suka zaga ƙasashen Edom da Mowab, suka wuce ta gabashin ƙasar Mowab, sa’an nan suka yi sansani a ɗaya gefen Arnon. Ba su shiga yankin Mowab ba, gama Arnon ce iyakarta.

  6. Ka fi Balak ɗan Ziffor, sarkin Mowab ne? Ka taɓa ji ya yi hamayya da Isra’ila ko yă yi yaƙi da su?

  7. A kwanakin da mahukunta suke mulki an yi yunwa a ƙasar, sai wani mutum daga Betlehem a Yahuda tare da matarsa da ’ya’yansu maza biyu, suka tafi su yi zama na ɗan lokaci a ƙasar Mowab.

  8. Sunan mutumin, Elimelek ne, sunan matarsa Na’omi; sunayen ’ya’yan nan nasu biyu, su ne Malon da Kiliyon. Su Efratawa ne daga Betlehem ta Yahuda. Suka kuwa tafi Mowab suka zauna a can.

  9. Suka auri mata Mowabawa, sunan ɗaya Orfa ɗayan kuma Rut. Bayan sun zauna a can kamar shekara goma,

  10. Sa’ad da ta ji a Mowab cewa Ubangiji ya zo don yă taimaki mutanensa ta wurin tanada musu da abinci, sai Na’omi tare da surukanta suka shirya su koma gida daga can.

  11. Na’omi fa ta koma daga Mowab tare da Rut mutuniyar Mowab, surukarta, suka kai Betlehem a lokacin da ake fara girbin sha’ir.

  12. Shugaban ya amsa, “Ita ce mutuniyar Mowab da ta zo daga Mowab tare da Na’omi.

  13. Sa’an nan ya ce wa dangin nan mai fansa, “Na’omi, wadda ta dawo daga Mowab, tana so ta sayar da filin da yake na ɗan’uwanmu Elimelek.

  14. Amma suka manta da Ubangiji Allahnsu, shi kuma ya bashe su a hannun Sisera shugaban rundunar Hazor da kuma hannun Filistiyawa da sarkin Mowab wanda suka yi yaƙi da su.

  15. Bayan Shawulu ya hau karagar mulkin Isra’ila, ya yi yaƙi da abokan gābansu ta kowane gefe. Mowabawa, Ammonawa, mutanen Edom, sarakunan Zoba, da kuma Filistiyawa. Duk wurin da ya juya, ya hore su.

  16. Daga can Dawuda ya tafi Mizfa a Mowab. Ya ce wa sarkin Mowab, “Za ka yarda mahaifina da mahaifiyata su zo su zauna a wurinka kafin in san abin da Allah zai yi da ni?”

  17. Saboda haka ya bar su a wurin sarkin Mowab, suka zauna da shi duk tsawon lokacin da Dawuda yake ta ɓuya a kogwannin duwatsu.

  18. Haka kuma Dawuda ya ci Mowabawa. Ya sa suka kwanta a ƙasa, ya kuma auna su da igiya. Kowane awo biyu ya sa a kashe su, amma awo na uku sai yă sa a bar su da rai. Saboda haka Mowabawa suka zama bayin Dawuda, suka kuma kawo masa haraji.

  19. wato, azurfa da zinariyan mutanen Edom, da na Mowabawa, da na Ammonawa, da na Filistiyawa, da na Amalekawa, da ganimar Hadadezer ɗan Rehob, sarkin Zoba.

  20. Benahiya, ɗan Yehohiyada mutumin Kabzeyel shi ma jarumi ne sosai, ya yi nasarori masu yawa. Ya bugi ƙwararrun jarumawan Mowab guda biyu. Ya kuma shiga rami wata ranar da ake ƙanƙara, ya kashe zaki.

  21. A kan tudu, gabas da Urushalima, Solomon ya gina masujada a can domin Kemosh, allahn da aka hana na Mowab, da Molek, allahn da aka hana na Ammonawa.

  22. Bayan mutuwar Ahab, Mowab ta yi wa Isra’ila tawaye.

  23. Mesha, sarkin Mowab yana kiwon tumaki, ya kuma zama tilas yă biya haraji ga sarkin Isra’ila. Saboda haka yakan ba da ’yan tumaki dubu ɗari, da kuma gashin raguna dubu ɗari.

  24. Amma bayan mutuwar Ahab, sai sarkin Mowab ya yi wa sarkin Isra’ila tawaye.

  25. Ya kuma aika da wannan saƙo ga Yehoshafat sarkin Yahuda cewa, “Sarkin Mowab ya yi mini tawaye. Za ka tafi tare da ni mu yaƙi Mowab?” Sai sarkin Yahuda ya ce, “I, ina shirye mu tafi. Ai, sojojina sojojinka ne, dawakaina kuma dawakanka ne.”