Tsallake zuwa abun ciki

Jesus

3,872 ayoyi · 6 'yan gida

An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ

Ayoyin da suka ambaci Jesus

Tace bisa littafi
  1. Daga haihuwa an jefa ni a kanka; daga cikin mahaifiyata kai ne Allahna.

  2. Kada ka yi nesa da ni, gama wahala na kusa kuma babu wani da zai taimaka.

  3. Bijimai masu yawa sun kewaye ni; bijimai masu ƙarfi na Bashan sun sa ni a tsaka.

  4. Zakoki masu ruri suna yayyage abin da suka kama sun buɗe bakunansu a kaina.

  5. An zubar da ni kamar ruwa, kuma dukan ƙasusuwana sun fiffito daga mahaɗai. Zuciyata ta zama kaki; ta narke a cikina.

  6. Ƙarfina ya bushe kamar kasko, harshena kuma ya manne wa dasashina na sama; ka kwantar da ni a ƙurar mutuwa.

  7. Karnuka sun kewaye ni; ƙungiyar mugaye sun sa ni a tsaka, sun soki hannuwana da ƙafafuna.

  8. Zan iya ƙirga ƙasusuwana; mutane suna farin ciki a kaina.

  9. Sun raba rigunana a tsakaninsu suka kuma jefa ƙuri’a a kan rigunana.

  10. Amma kai, ya Ubangiji, kada ka yi nisa; Ya Ƙarfina zo da sauri don ka taimake ni.

  11. Ka ceci raina daga takobi, raina mai daraja daga ikon karnuka.

  12. Ka cece ni daga bakin zakoki; ka cece ni daga ƙahonin ɓauna.

  13. Zan furta sunanka ga ’yan’uwana; cikin taron masu sujada zan yabe ka.

  14. Daga gare ka yabona yake zuwa cikin babban taro; a gaban waɗanda suke tsoronka zan cika alkawarina.

  15. Ka san yadda ake mini ba’a, ake kunyatar da ni da kuma yadda nake shan kunya; dukan abokan gābana suna a gabanka.

  16. Zai yi kira gare ni yă ce, ‘Kai ne Mahaifina, Allahna, Dutse mai cetona.’

  17. Zan kuma naɗa shi ɗan farina, mafi ɗaukaka cikin sarakunan duniya.

  18. Ta Dawuda. Zabura ce. Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana, sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.”

  19. Ubangiji zai fadada ikon sandan mulkinka daga Sihiyona za ka yi mulki a tsakiyar abokan gābanka.

  20. Ubangiji ya rantse ba zai kuma canja zuciyarsa ba, “Kai firist ne har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.”

  21. Ubangiji yana a hannun damanka; zai murƙushe sarakuna a ranar fushinsa.

  22. Zai hukunta al’ummai, yana tarawa gawawwaki yana kuma murƙushe masu mulkin dukan duniya.

  23. Zai sha daga rafin da yake kusa da hanya; saboda haka zai ɗaga kansa sama.

  24. Ubangiji ya rantse wa Dawuda tabbataccen rantsuwa cewa ba zai janye ba cewa, “Ɗaya daga cikin zuriyarka zan sa a kan kursiyinka,

  25. Wane ne ya taɓa haura zuwa sama ya dawo? Wane ne ya tattara iska a tafin hannuwansa? Wane ne ya nannaɗe ruwaye a cikin rigarsa? Wane ne ya kafa dukan iyakokin duniya? Mene ne sunansa, da kuma sunan ɗansa? Faɗa mini in ka sani!