Tsallake zuwa abun ciki

Jesus

3,872 ayoyi · 6 'yan gida

An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ

Ayoyin da suka ambaci Jesus

Tace bisa littafi
  1. Filibus ya gangara zuwa wani birni a Samariya ya kuma yi shelar Kiristi a can.

  2. Amma da suka gaskata da Filibus sa’ad da yake wa’azin labari mai daɗi na mulkin Allah da kuma sunan Yesu Kiristi, sai aka yi musu baftisma, maza da mata.

  3. domin Ruhu Mai Tsarki bai riga ya sauka wa waninsu ba tukuna, an dai yi musu baftisma ne kawai a cikin sunan Ubangiji Yesu.

  4. Sai Siman ya amsa ya ce, “Ku yi addu’a ga Ubangiji saboda ni don kada ko ɗaya daga cikin abin da ka faɗa ya same ni.”

  5. Sa’ad da suka yi shaidar suka kuma yi shelar maganar Ubangiji, sai Bitrus da Yohanna suka koma Urushalima, suna wa’azin bishara a ƙauyukan Samariya masu yawa.

  6. To wani mala’ikan Ubangiji ya ce wa Filibus, “Ka yi kudu zuwa hanyar, hanyar hamada, da ta gangara daga Urushalima zuwa Gaza.”

  7. Bābān yana karanta wannan Nassin, “An ja shi kamar tunkiya zuwa mayanka, kuma kamar ɗan rago a hannun mai askin gashinsa yake shiru, haka kuwa bai buɗe bakinsa ba.

  8. A cikin wulaƙacinsa aka hana masa gaskiya. Wa zai iya yin zancen zuriyarsa? Gama an ɗauke ransa daga duniya.”

  9. Sa’an nan Filibus ya fara da wannan Nassi ɗin ya kuma faɗa masa labari mai daɗi game da Yesu.

  10. And Philip said, If thou believest with all thine heart, thou mayest. And he answered and said, I believe that Jesus Christ is the Son of God.

  11. Sa’ad da suka fita daga cikin ruwan, sai Ruhun Ubangiji ya fyauce Filibus, bābān kuwa bai ƙara ganinsa ba, amma ya ci gaba da tafiyarsa yana farin ciki.

  12. Ana cikin haka, Shawulu ya ɗage yana barazana yin kisa da tsananta wa almajiran Ubangiji. Sai ya je wurin babban firist

  13. Sai ya fāɗi a ƙasa ya kuma ji wata murya ta ce masa, “Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini?”

  14. Shawulu ya yi tambaya ya ce, “Wane ne kai, ya Ubangiji?” Ya amsa ya ce, “Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.

  15. Yanzu ka tashi ka shiga cikin birnin, za a kuma gaya maka abin da dole za ka yi.”

  16. A Damaskus kuwa akwai wani almajiri mai suna Ananiyas. Ubangiji ya kira shi a cikin wahayi ya ce, “Ananiyas!” Ananiyas ya amsa, “Ga ni, ya Ubangiji.”

  17. Ubangiji ya ce masa, “Je gidan Yahuda da yake a Miƙaƙƙen Titi ka yi tambaya ko akwai wani mutum daga Tarshish mai suna Shawulu, gama ga shi yana addu’a.

  18. Ananiyas ya amsa ya ce, “Ubangiji, na ji labarin mutumin nan sosai da kuma duk lahanin da ya yi wa tsarkakanka a Urushalima.

  19. Ga shi kuma ya zo nan da izinin manyan firistoci, don yă kama duk wanda yake kiran bisa sunanka.”

  20. Amma Ubangiji ya ce wa Ananiyas, “Je ka! Wannan mutum zaɓaɓɓen kayan aikina ne don yă kai sunana a gaban Al’ummai da sarakunansu da kuma a gaban mutanen Isra’ila.

  21. Zan nuna masa wahalar da dole zai sha saboda sunana.”

  22. Sa’an nan Ananiyas ya tafi gidan ya kuma shiga ciki. Da ya sa hannuwansa a kan Shawulu, sai ya ce, “Ɗan’uwana Shawulu, Ubangiji, Yesu, wanda ya bayyana gare ka a kan hanya yayinda kake zuwa nan, ya aiko ni domin ka sāke gani a kuma cika ka da Ruhu Mai Tsarki.”

  23. Nan take ya fara wa’azi cikin majami’u cewa Yesu Ɗan Allah ne.

  24. Duk da haka Shawulu ya yi ta ƙara ƙarfi, ya kuma rikitar da Yahudawan da suke zaune a Damaskus, ta wurin tabbatar musu cewa, Yesu shi ne Kiristi.

  25. Amma Barnabas ya ɗauke shi ya kawo shi wurin manzanni. Ya gaya musu yadda Shawulu a kan hanyarsa ya ga Ubangiji kuma cewa Ubangiji ya yi magana da shi, da yadda a Damaskus ya yi wa’azi ba tsoro a cikin sunan Yesu.