Tsallake zuwa abun ciki

Jesus

3,872 ayoyi · 6 'yan gida

An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ

Ayoyin da suka ambaci Jesus

Tace bisa littafi
  1. Allah ya ɗaukaka shi zuwa hannun damansa a matsayin Yerima da Mai Ceto don yă kawo tuba da gafarar zunubai ga Isra’ila.

  2. Mu shaidu ne ga waɗannan abubuwa, haka kuma Ruhu Mai Tsarki, wanda Allah ya ba wa waɗanda suke yin masa biyayya.”

  3. Jawabinsa ya rinjaye su. Suka kira manzannin suka sa aka yi musu bulala. Sa’an nan suka kwaɓe su kada su ƙara magana a cikin sunan Yesu, suka kuma bar su suka tafi.

  4. Manzannin suka bar Majalisar, suna farin ciki domin an ga sun cancanta a kunyata su saboda Sunan nan.

  5. Kowace rana, a filin haikali da kuma gida-gida, ba su fasa koyarwa da kuma shelar labari mai daɗi cewa Yesu shi ne Kiristi ba.

  6. Gama mun ji shi yana cewa wannan Yesu Banazare zai rushe wurin nan ya kuma canja al’adun da Musa ya ba mu.”

  7. Bai ba shi gādo a nan ba, ko taki ɗaya na ƙasa. Amma Allah ya yi masa alkawari cewa shi da zuriyarsa masu zuwa bayansa za su mallaki ƙasar, ko da yake a lokacin Ibrahim ba shi da yaro.

  8. Amma zan hore ƙasar da suka bauta wa.’ Allah ya ce, ‘Kuma daga baya za su fita daga wannan ƙasa su kuma yi mini sujada a wannan wuri.’

  9. Sa’an nan ya yi wa Ibrahim alkawari game da kaciya. Ibrahim kuwa ya zama mahaifin Ishaku ya kuma yi masa kaciya kwana takwas bayan haihuwarsa. Daga baya Ishaku ya zama mahaifin Yaƙub, Yaƙub kuma ya zama mahaifin kakanninmu sha biyun nan.

  10. “Bayan shekaru arba’in suka wuce, sai mala’ika ya bayyana ga Musa cikin harshen wuta a ɗan itace a hamada kusa da Dutsen Sinai.

  11. Sa’ad da ya ga haka, ya yi mamakin abin da ya gani. Da ya yi kusa domin ya duba sosai, sai ya ji muryar Ubangiji ta ce,

  12. “Sa’an nan Ubangiji ya ce masa, ‘Ka cire takalmanka; wurin da kake tsayen nan mai tsarki ne.

  13. “Wannan Musa ɗin da suka ƙi suna cewa, ‘Wa ya mai da kai mai mulki da kuma alƙali?’ Allah da kansa ya aike shi, ta wurin mala’ikan da ya bayyana a gare shi a ɗan itace, yă zama mai mulkinsu, da kuma mai cetonsu.

  14. “Wannan Musa ne ya ce Isra’ilawa, ‘Allah zai aika muku wani annabi kamar ni daga cikin mutanenku.’

  15. Ya kasance a cikin taron nan a hamada, tare da mala’ikan da ya yi magana da shi a Dutsen Sinai, da kuma tare da kakanninmu; ya kuma karɓi kalmomi masu rai don yă miƙa mana.

  16. Sai Amma Allah ya juya musu baya ya kuma ba da su ga bautar abubuwan da suke a sararin sama. Wannan ya yi daidai da abin da yake a rubuce a cikin littafin annabawa cewa, “ ‘Kun kawo mini hadayu da sadakoki shekaru arba’in cikin, hamada, ya gidan Isra’ila?

  17. “Kakanni-kakanninmu suna da tabanakul na Shaida tare da su a hamada. An yi shi bisa ga yadda Allah ya umarci Musa, bisa ga zānen da ya gani.

  18. Amma Solomon ne ya gina masa gida.

  19. “Duk da haka, Mafi Ɗaukaka ba ya zama a gidajen da mutane suka gina. Kamar yadda annabi ya faɗi cewa,

  20. “ ‘Sama ne kursiyina, duniya kuma wurin ajiye tafin ƙafata. Wane irin gida za ka gina mini? Ko kuwa ina wurin hutuna zai kasance? In ji Ubangiji.

  21. Ba hannuna ne ya yi dukan waɗannan abubuwa ba?’

  22. Amma Istifanus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dubi sama ya kuma ga ɗaukakar Allah, da Yesu kuma tsaye a hannun dama na Allah.

  23. Ya ce, “Ga shi, na ga sama a buɗe da kuma Ɗan Mutum tsaye a hannun dama na Allah.”

  24. Yayinda suke cikin jifansa, sai Istifanus ya yi addu’a ya ce, “Ubangiji Yesu, ka karɓi ruhuna.”

  25. Sa’an nan ya durƙusa ya ɗaga murya ya ce, “Ubangiji, kada ka riƙe wannan zunubi a kansu.” Da ya faɗi haka, sai ya yi barci.