Tsallake zuwa abun ciki

Israel

1,007 ayoyi · 20 'yan gida

An kuma san shi da: Jacob

Ayoyin da suka ambaci Israel

Tace bisa littafi
  1. Haka Musa ya ƙidaya ’ya’yan fari na Isra’ilawa, yadda Ubangiji ya umarce shi.

  2. “Ka ɗauki Lawiyawa a maimakon dukan ’ya’yan fari na Isra’ila, dabbobin Lawiyawa kuma a maimakon dabbobinsu. Lawiyawa za su zama nawa. Ni ne Ubangiji.

  3. Don a fanshi ’ya’yan fari 273 na Isra’ilawa da suka fi Lawiyawa yawa,

  4. Daga ’ya’yan fari na Isra’ilawa, ya karɓi azurfa masu nauyin shekel 1,365, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri.

  5. “Ka umarci Isra’ilawa su kori duk wanda yake da ciwon fatan jiki, ko mai ɗiga na kowane iri, ko wanda ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, daga cikin sansani.

  6. Isra’ilawa suka yi haka; suka kore su daga sansanin. Suka aikata yadda dai Ubangiji ya umarci Musa.

  7. “Gaya wa Isra’ilawa, ‘Sa’ad da namiji ko mace ya yi wa ɗan’uwansa laifi ta kowace hanya, ta yin haka, ya yi rashin aminci ga Ubangiji, mutumin kuwa ya yi laifi ke nan

  8. Dukan tsarkakakkun abubuwan da Isra’ilawa suka kawo wa firist za su zama nasa.

  9. “Yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘In matar wani ta kauce, ta kuma yi rashin aminci gare shi

  10. “Yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘In mace, ko namiji yana so yă yi alkawari na musamman, alkawarin zaman keɓaɓɓe ga Ubangiji, a matsayin Banazare,

  11. “Gaya wa Haruna da ’ya’yansa, ‘Ga yadda za ku albarkaci Isra’ilawa. Za ku ce musu,

  12. “Da haka za su sa sunana a kan Isra’ilawa, ni kuma zan albarkace su.”

  13. “Keɓe Lawiyawa daga sauran Isra’ilawa, ka tsarkake su.

  14. Ka kawo Lawiyawa a gaban Tentin Sujada, ka kuma kira taron Isra’ilawa duka.

  15. Za ka kawo Lawiyawa a gaban Ubangiji, Isra’ilawa kuma za su ɗibiya musu hannuwansu.

  16. Haruna zai miƙa Lawiyawa a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa daga Isra’ilawa, saboda a shirya su domin aikin Ubangiji.

  17. Da haka za ka keɓe Lawiyawa daga sauran Isra’ilawa, Lawiyawa za su zama nawa.

  18. Gama dukansu an ba ni su daga cikin Isra’ilawa a maimakon dukan waɗanda suka fara buɗe mahaifa, wato, dukan ’ya’yan farin Isra’ilawa. Na karɓi Lawiyawa su zama nawa.

  19. Kowane ɗan farin haihuwa, ko mutum, ko dabba a Isra’ila, nawa ne. Sa’ad da na kashe ’ya’yan fari a Masar, na keɓe ’ya’yan fari na Isra’ilawa wa kaina.

  20. Na kuma ɗauki Lawiyawa a maimakon dukan ’ya’yan fari maza a Isra’ila.

  21. Cikin dukan Isra’ilawa, na ba da Lawiyawa kyauta ga Haruna da ’ya’yansa, su yi hidima a Tentin Sujada a madadin Isra’ilawa, su kuma yi kafara dominsu saboda kada annoba ta bugi Isra’ilawa sa’ad da suka je kusa da wuri mai tsarki.”

  22. Musa, Haruna da kuma dukan taron Isra’ilawa, suka yi da Lawiyawa yadda Ubangiji ya umarci Musa.

  23. “Ka sa Isra’ilawa su yi Bikin Ƙetarewa a ƙayyadadden lokaci.

  24. Saboda haka sai Musa ya gaya wa Isra’ilawa su yi Bikin Ƙetarewa,

  25. suka kuwa yi haka a Hamadar Sinai da yamma, a rana ta sha huɗu ga watan farko. Isra’ilawa suka yi dukan abubuwa yadda Ubangiji ya umarci Musa.