Tsallake zuwa abun ciki

Israel

1,007 ayoyi · 20 'yan gida

An kuma san shi da: Jacob

Ayoyin da suka ambaci Israel

Tace bisa littafi
  1. “Yi magana da Haruna da ’ya’yansa maza da kuma dukan Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji ya umarta.

  2. Duk mutumin Isra’ilan da ya yanka sa, ɗan rago ko akuya a sansani ko waje da shi

  3. Wannan ya zama haka saboda Isra’ilawa su kawo wa Ubangiji hadayun da suke yi a filaye. Dole su kawo su ga firist, wato, ga Ubangiji, a ƙofar Tentin Sujada, su miƙa su a matsayin hadayun salama.

  4. “Faɗa musu, ‘Duk wani mutumin Isra’ila ko wani baƙon da yake zama a cikinsu wanda ya miƙa hadaya ta ƙonawa ko sadaka

  5. “ ‘Duk mutumin Isra’ila ko baƙon da yake zama a cikinsu wanda ya ci wani jini, zan yi gāba da wannan mutum wanda ya ci jinin, za a kuma raba shi da mutanensa.

  6. Saboda haka na ce wa Isra’ilawa, “Babu waninku da zai ci jini, babu wani baƙon da yake zama a cikinku da zai ci jini.”

  7. “ ‘Duk wani mutumin Isra’ila ko baƙon da yake zama a cikinku wanda ya ji wa wani dabba ko tsuntsu wanda ake ci ciwo, dole yă tsiyaye jinin yă rufe shi da ƙasa,

  8. domin ran kowace halitta yana cikin jini. Shi ya sa na ce wa Isra’ilawa, “Kada ku ci jinin wani halitta, domin ran kowace halitta yana cikin jinin; duk wanda ya ci shi dole a fid da shi.”

  9. “Yi wa Isra’ilawa magana ka kuma faɗa musu cewa, ‘Ni ne Ubangiji Allahnku.

  10. “Yi wa taron jama’ar Isra’ila gaba ɗaya magana, ka ce musu, ‘Ku zama masu tsarki, domin Ni, Ubangiji Allahnku, mai tsarki ne.

  11. “Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘Duk wani mutumin Isra’ila ko baƙon da yake zama a cikin Isra’ila da ya miƙa wani daga cikin ’ya’yansa wa Molek, dole sa kashe shi. Mutanen ƙasar za su jajjefe shi.

  12. Sai Musa ya faɗa wannan wa Haruna da ’ya’yansa maza da kuma dukan Isra’ilawa.

  13. “Faɗa wa Haruna da ’ya’yansa maza, su lura da tsarkakakkun abubuwan da Isra’ilawa suka keɓe gare ni da bangirma, saboda ba za su ƙazantar da sunana mai tsarki ba. Ni ne Ubangiji.

  14. “Faɗa musu cewa, ‘Don tsararraki masu zuwa, in wani zuriyarku ya ƙazantu, duk da haka ya kusaci tsarkakakku hadayun da Isra’ilawa suka keɓe ga Ubangiji, dole a raba wannan mutum daga gabana. Ni ne Ubangiji.

  15. Firist ɗin ba zai ƙasƙantar da tsarkakakkun hadayun da Isra’ilawa suka kawo ga Ubangiji

  16. “Yi wa Haruna da ’ya’yansa maza da kuma dukan Isra’ilawa magana ka ce musu, ‘In waninku, ko mutumin Isra’ila, ko baƙon da yake zama a Isra’ila, ya kawo kyauta don hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, ko don yă cika alkawari, ko kuwa a matsayin hadaya ta yardar rai,

  17. Kada ku ƙasƙantar da sunana mai tsarki. Dole Isra’ilawa su gane Ni mai tsarki ne. Ni ne Ubangiji, wanda ya keɓe ku a matsayin tsarkaka

  18. “Yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Ga ƙayyadaddun bukukkuwa, ƙayyadaddun bukukkuwan Ubangiji, da za ku sanar wa mutane su riƙa kiyayewa, su zama lokutan tarurruka masu tsarki.

  19. “Yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar da zan ba ku, kuka kuma girbe amfanin gonarta, sai ku kawo wa firist damin hatsi na farko da kuka girbe.

  20. “Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘A ranar farko ga wata na bakwai, za tă zama ranar hutu, rana ce ta tuni da yin taro mai tsarki na sujada da za a fara busar ƙaho.

  21. “Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘A ranar goma sha biyar ga wata na bakwai, za a fara Bikin Tabanakul na Ubangiji, zai kuma ɗauki kwana bakwai.

  22. don zuriyarku tă san cewa na sa Isra’ilawa suka zauna a bukkoki sa’ad da na fitar da su daga Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ”

  23. Saboda haka Musa ya sanar wa Isra’ilawa ƙayyadaddun bukukkuwan Ubangiji.

  24. “Ka umarci Isra’ilawa su kawo tsabtataccen mai na zaitun da aka matse, don ƙuna fitilun yadda harshen wutar ba zai taɓa mutuwa ba.

  25. Za a shirya wannan gurasa a gaban Ubangiji kowane Asabbaci, a madadin Isra’ilawa a matsayin madawwamin alkawari.