Tsallake zuwa abun ciki

Israel

1,007 ayoyi · 20 'yan gida

An kuma san shi da: Jacob

Ayoyin da suka ambaci Israel

Tace bisa littafi
  1. Cikin tafiyar Isra’ilawa duka, sukan kama tafiyarsu ne a duk sa’ad da girgijen ya tashi daga kan tabanakul.

  2. Gama a cikin tafiyarsu duka, girgijen Ubangiji yana kan tabanakul da rana, da dare kuwa wuta yake cikinsa domin dukan Isra’ilawa su gani.

  3. “Yi magana da Isra’ilawa ka ce musu, ‘Duk sa’ad da waninku ya kawo hadaya ga Ubangiji, ku kawo hadayarku ta dabba daga garkenku ta shanu ko kuwa daga tumakinku.

  4. “Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘Sa’ad da wani ya yi zunubi ba da gangan ba, har ya karya ɗaya daga cikin dokokin Ubangiji,

  5. “ ‘In dukan jama’ar Isra’ilawa suka yi zunubi ba da gangan ba, har suka aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, ko da yake jama’ar ba su san batun ba, duk da haka sun yi laifi.

  6. “Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Kada ku ci wani kitsen shanu, ko na tumaki, ko kuwa na awaki.

  7. “Faɗa wa Isra’ilawa, ‘Duk wanda ya kawo hadaya ta salama ga Ubangiji, sai ya kawo hadayarsa ga Ubangiji daga cikin hadayu na salama.

  8. Daga hadaya ta salama ta Isra’ilawa, na ɗauki ƙirjin da aka kaɗa da kuma cinyar da aka miƙa, na ba da su ga Haruna firist da kuma ’ya’yansa maza a matsayin rabonsu na kullum daga Isra’ilawa.’ ”

  9. A ranar da aka keɓe su, Ubangiji ya umarta cewa Isra’ilawa su ba da wannan a gare su a matsayin rabonsu na kullum, a dukan tsararraki masu zuwa.

  10. waɗanda Ubangiji ya ba wa Musa a Dutsen Sinai, a Hamadar Sinai, a ranar da ya umarci Isra’ilawa su kawo hadayunsu ga Ubangiji.

  11. A rana ta takwas, Musa ya kira Haruna da ’ya’yansa maza da kuma dattawan Isra’ila.

  12. Sa’an nan ka ce wa Isra’ilawa, ‘Ku ɗauki bunsuru na yin hadaya don zunubi, da ɗan maraƙi bana ɗaya, da ɗan rago bana ɗaya marasa lahani, don hadaya ta ƙonawa,

  13. Sa’an nan Musa ya ce wa Haruna da Eleyazar da Itamar ’ya’yansa maza, “Kada ku bar gashin kanku barkatai, kada kuma ku yage tufafinku, don kada ku mutu. Yin haka zai jawo fushin Ubangiji a kan dukan jama’a. Amma dangoginku, wato, dukan Isra’ilawa, suna iya kuka saboda waɗanda Ubangiji ya hallaka da wuta.

  14. za ku kuma koyar da Isra’ilawa dukan farillan da Ubangiji ya ba su ta wurin Musa.”

  15. Amma kai da ’ya’yanka maza da mata za su iya ci ƙirjin da aka kaɗa, da kuma cinyar da aka miƙa. Ku ci su a wuri mai tsabta; an ba da su gare ku da kuma ’ya’yanku a matsayin rabo daga hadaya ta salama ta Isra’ilawa.

  16. “Ku ce wa Isra’ilawa, ‘Cikin dabbobin da suke a doron ƙasa, waɗannan ne za ku ci.

  17. “Faɗa wa Isra’ilawa, ‘Macen da ta yi ciki ta kuma haihu ɗa namiji za tă ƙazantu kwana bakwai, kamar yadda takan ƙazantu a lokacin al’adarta.

  18. “Yi wa Isra’ilawa magana, ku ce musu, ‘Duk sa’ad da wani namiji yake ɗiga daga azzakarinsa, wannan ɗiga marar tsarki ne.

  19. “ ‘Ta haka za ka tsarkake Isra’ilawa daga rashin tsarkinsu, domin kada su mutu saboda rashin tsarkinsu ta wurin ƙazantar da wurin zamana wanda yake tsakiyarsu.’ ”

  20. Zai ɗauki bunsurai biyu daga jama’ar Isra’ilawa na hadaya don zunubi da ɗan rago don hadaya ta ƙonawa.

  21. Ta haka zai yi kafara domin Wuri Mafi Tsarki saboda ƙazantar tawayen Isra’ilawa, da laifofinsu, da dukan zunubansu. Haka zai yi saboda Tentin Sujada wanda yake a cikinsu a tsakiyar ƙazantarsu.

  22. Kada kowa yă kasance a Tentin Sujada daga lokacin da Haruna ya shiga don yă yi kafara a Wuri Mafi Tsarki har sai ya fita, bayan ya yi kafara domin kansa, gidansa da kuma dukan jama’ar Isra’ila.

  23. Zai yayyafa jinin a kan bagade da yatsarsa sau bakwai, yă tsabtacce shi yă kuma tsarkake shi daga ƙazantar Isra’ilawa.

  24. Haruna zai ɗibiya hannuwansa a kan akuya mai ran, yă furta a kansa dukan mugunta da tawayen Isra’ilawa, dukan zunubansu, yă kuma sa su a kan akuyan. Zai kori akuyan zuwa cikin jeji a hannun mutumin da aka ba shi aikin yin haka.

  25. “Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ce gare ku. Za a riƙa yin kafara sau ɗaya a shekara saboda dukan zunuban Isra’ilawa.” Aka kuma yi haka, yadda Ubangiji ya umarci Musa.