Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Game da Ishmayel kuwa, na ji ka. Tabbatacce zan albarkace shi, zan sa yă azurta, zai kuma ƙaru ƙwarai. Zai zama mahaifin masu mulki goma sha biyu, zan kuma maishe shi babban al’umma!

  2. Amma dai zan kafa alkawarina da Ishaku wanda Saratu za tă haifa maka war haka shekara mai zuwa.”

  3. Da ya gama magana da Ibrahim, sai Allah ya tashi daga gare shi.

  4. A wannan rana, Ibrahim ya ɗauki ɗansa Ishmayel da dukan waɗanda aka haifa cikin gidansa, da waɗanda aka sayo da kuɗinsa, ya kuwa yi wa kowane namiji a cikin gidansa kaciya kamar yadda Allah ya faɗa masa.

  5. Ubangiji ya bayyana ga Ibrahim kusa da manyan itatuwan Mamre yayinda yake zaune a mashigin tentinsa da tsakar rana.

  6. Ya ce, “Ranka yă daɗe, in na sami tagomashi daga gare ku kada ku wuce bawanku.

  7. Bari a kawo ruwa ku wanke ƙafafunku, ku huta a ƙarƙashin wannan itace.

  8. Bari in samo muku wani abu ku ci don ku wartsake, sa’an nan ku ci gaba da tafiyarku; da yake kun biyo wurin bawanku.” Suka ce, “To, sai ka yi abin da ka ce.”

  9. Sa’an nan ɗayansu ya ce, “Lalle zan komo wurinka war haka shekara mai zuwa. Saratu matarka kuwa za tă haifi ɗa.” Saratu kuwa tana a bayansu tana ji daga mashigin tenti.

  10. Sai Ubangiji ya ce wa Ibrahim, “Me ya ba Saratu dariya har da ta ce, ‘Har zan iya haifi ɗa duk ta tsufata yanzu?’

  11. Akwai abin zai gagari Ubangiji? Zan komo wurinka a ƙayyadadden lokacin nan shekara mai zuwa kuma Saratu za tă haifi ɗa.”

  12. Saratu ta ji tsoro, don haka sai ta yi ƙarya ta ce, “Ban yi dariya ba.” Ya ce, “A’a, kin yi dariya.”

  13. Sai Ubangiji ya ce, “Zan ɓoye wa Ibrahim abin da nake shirin yi?

  14. Saboda na zaɓe shi don yă umarci ’ya’yansa da iyalinsa a bayansa su kiyaye hanyoyin Ubangiji, ta wurin yin abin da yake daidai da kuma yin adalci, domin Ubangiji ya aikata abin da ya yi wa Ibrahim alkawari.”

  15. Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Kuka a kan Sodom da Gomorra ta yi yawa, zunubinsu kuma ya yi muni sosai,

  16. zan gangara in ga ko abin da suka yi ya yi muni kamar yadda kukan ya zo gare ni, zan bincike.”

  17. Sai mutanen suka juya suka nufi wajen Sodom amma Ibrahim ya ci gaba da kasance a gaban Ubangiji.

  18. Sai Ibrahim ya matso wurinsa ya ce, “Za ka hallaka masu adalci tare da masu mugunta?

  19. Tabbatacce ba za ka taɓa aikata irin wannan abu ba, ka kashe masu adalci tare da masu mugunta, ka ɗauka masu adalci da masu mugunta daidai? Tabbatacce ba za ka taɓa aikata irin wannan abu ba! Mai hukuncin dukan duniya ba zai aikata gaskiya ba?”

  20. Ubangiji ce, “In na sami mutum hamshin masu adalci a cikin birnin Sodom, zan bar dukan birnin saboda su.”

  21. Sai Ibrahim ya ƙara cewa, “Yanzu da na yi karambani har na yi magana da Ubangiji, ko da yake ni ba kome ba ne illa turɓaya da toka,

  22. in yawan masu adalci sun kāsa hamshin da mutum biyar fa? Za ka hallaka dukan birnin saboda rashin mutum biyar ɗin?” Ya ce, “In na sami mutum arba’in da biyar a wurin, ba zan hallaka shi ba.”

  23. Ya sāke cewa, “In mutum arba’in kaɗai aka samu a can fa?” Ya ce, “Saboda mutum arba’in ɗin, ba zan aikata ba.”

  24. Sai ya ce, “Kada Ubangiji ya yi fushi, amma bari in ƙara magana. A ce mutum talatin kaɗai aka samu a can fa?” Ya ce, “Ba zan aikata ba, in na sami mutum talatin a can.”

  25. Ibrahim ya ce, “Yanzu fa da na yi karambani har na yi magana da Ubangiji, in ashirin kaɗai aka samu a can fa?” Ya ce, “Saboda ashirin ɗin, ba zan hallaka shi ba.”