Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Cewa in ka furta da bakinka, “Yesu Ubangiji ne,” ka kuma gaskata a zuciyarka cewa Allah ya tā da shi daga matattu, za ka sami ceto.

  2. Saboda haka, bangaskiya takan zo ne ta wurin jin saƙo, akan ji saƙon kuma ta wurin maganar Kiristi.

  3. To, ina da tambaya. Allah ya ƙi mutanensa ne? Sam, ko kaɗan! Ni mutumin Isra’ila ne kaina, zuriyar Ibrahim kuwa, daga kabilar Benyamin.

  4. Allah bai ƙi mutanensa da ya rigya sani ba. Ba ku san abin da Nassi ya faɗa game da Iliya ba, yadda ya kawo kuka ga Allah a kan Isra’ila ya ce,

  5. Wace amsa ce Allah ya ba shi? “Na keɓe wa kaina dubu bakwai waɗanda ba su yi wa Ba’al sujada ba.”

  6. kamar yadda yake a rubuce cewa, “Allah ya ba su ruhun ruɗewa, idanu don su kāsa gani, da kuma kunnuwa don su kāsa ji, har yă zuwa yau.”

  7. Har yanzu ina da tambaya. Sun yi tuntuɓe har ya kai ga fāɗuwar da ba za su iya tashi ba ne? Sam, ko kaɗan! A maimako, saboda laifinsu ne ceto ya zo ga Al’ummai don a sa mutanen Isra’ila su ji kishi.

  8. Gama in har Allah bai bar rassan nan na asali ba, kai ma ba zai bar ka ba.

  9. Ka lura fa da alheri da kuma tsananin Allah, tsanani ga waɗanda suka fāɗi, amma alheri a gare ka, da fata za ka ci gaba cikin alherinsa. In ba haka ba, kai ma za a sare ka.

  10. In kuwa ba su nace cikin rashin bangaskiya ba, za a sāke ɗaura aure da su, domin Allah yana iya sāke haɗa su.

  11. gama kyautar Allah da kiransa ba a sokewa.

  12. Kamar yadda a dā can ku da kuke marasa biyayya ga Allah kuka sami jinƙai yanzu ta dalilin rashin biyayyarsu,

  13. Gama Allah ya daure dukan mutane ga rashin biyayya don yă nuna jinƙai ga kowa.

  14. Kai, zurfin yalwar hikima da kuma sanin Allah yana nan a yalwace! Hukunce-hukuncensa kuma su fi gaban bincike, hanyoyinsa kuwa sun wuce gaban ganewa!

  15. Saboda haka, ina roƙonku, ’yan’uwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah, wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya.

  16. Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.

  17. Gama ta wurin alherin nan da aka yi mini ne ina ce wa kowannenku. Kada yă ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, a maimakon haka bari yă auna kansa cikin natsuwa, gwargwadon baiwar bangaskiyar da Allah yi masa.

  18. Dole kowa yă yi biyayya ga masu mulki, gama babu wani iko sai ko in Allah ya yarda. Duk hukumomin da muke su, naɗin Allah ne.

  19. Saboda haka, duk wanda ya yi tawaye ga hukuma yana yin tawaye da abin da Allah ya naɗa ne, waɗanda kuwa suke aikata haka, za su jawo wa kansu hukunci.

  20. Gama shi bawan Allah ne don kyautata rayuwarka. Amma in ka aikata mugunta, to, sai ka ji tsoro, don ba a banza ne shugaba yake ɗaukan takobinsa ba. Shi fa bawan Allah ne, ta wurinsa ne fushin Allah yakan hukunta masu laifi.

  21. Shi ne ma ya sa kuke biyan haraji, gama hukumomin nan bayin Allah ne, waɗanda suke ba da dukan lokacinsu don aikin shugabanci.

  22. Mutumin da yake cin kowane irin abinci, kada yă rena wanda ba ya cin, wanda kuma ba ya cin kowane irin abinci, kada yă ga laifin mutumin da yake ci, domin Allah ya riga ya karɓe shi.

  23. Kai wane ne har da za ka ga laifin bawan wani? Ko bawan yă yi aiki mai kyau, ko yă kāsa, ai, wannan ruwan maigidansa ne. Za a ma tsai da shi, domin Ubangiji yana da ikon tsai da shi.

  24. Wannan mai ɗaukan rana ɗaya da muhimmanci fiye da sauran, yana yin haka ne ga Ubangiji. Wannan mai cin nama, yana yin haka ne ga Ubangiji, gama yakan yi godiya ga Allah; wannan da ba ya ci kuwa, yana yin haka ne ga Ubangiji yana kuwa yin godiya ga Allah.

  25. In muna rayuwa, muna rayuwa ne ga Ubangiji; in kuma muna mutuwa, muna mutuwa ne ga Ubangiji. Saboda haka, ko muna a raye ko muna a mace, mu na Ubangiji ne.