Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Ƙaramin ya ce wa mahaifinsu, ‘Baba, ba ni rabon gādona.’ Sai mahaifin ya raba musu dukiyarsa.

  2. Zan tashi in koma wurin mahaifina, in ce masa, “Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi.

  3. “Sai ɗan ya ce masa, ‘Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi. Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba.’

  4. “Babu wani bawa mai iya bauta wa iyayengiji biyu ba. Ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗayan, ko kuwa ya dāge ga yi wa ɗaya bauta, sa’an nan ya rena ɗayan. Ba za ku iya ku bauta wa Allah tare da bauta wa Mammon (wato, Kuɗi) a lokaci ɗaya ba.”

  5. Ya ce musu, “Ku ne masu mai da kanku marasa laifi a gaban mutane, amma Allah ya san zuciyarku. Abu mai daraja a gaban mutane, abin ƙyama ne a gaban Allah.

  6. “An yi shelar Doka da Annabawa har zuwa lokacin Yohanna. Tun daga lokacin nan, bisharar mulkin Allah ne ake wa’azinta, kowa kuma yana ƙoƙarin kutsa kai ya shiga.

  7. Sai ya yi masa kira ya ce, ‘Baba, Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiki Lazarus ya sa ɗan yatsarsa a ruwa, ya ɗiga mini a harshe saboda in ji sanyi, domin ina shan azaba cikin wannan wuta.’

  8. Da ɗayansu ya ga ya warke, sai ya koma, yana yabon Allah da babbar murya.

  9. Ba wanda ya dawo don yă yabi Allah, sai dai wannan baƙon?”

  10. Wata rana, Farisiyawa suka tambaye shi lokacin da mulkin Allah zai zo, Yesu ya amsa ya ce, “Ai, mulkin Allah ba takan zo ta wurin yin kallon ku ba.

  11. Mutane kuma ba za su ce, ‘Ga shi nan,’ ko kuma, ‘Ga shi can’ ba, domin mulkin Allah yana cikinku ne.”

  12. Ya ce, “A wani gari, an yi wani alƙali wanda ba ya tsoron Allah, bai kuma kula da mutane ba.

  13. “An daɗe yana ƙi, amma a ƙarshe ya ce cikin tunaninsa, ‘Ko da yake ba na tsoron Allah, ba na kuma kula da mutane ba,

  14. Ashe, Allah ba zai biya wa zaɓaɓɓunsa da suke masa kuka, dare da rana adalci ba? Zai ci gaba da ƙin sauraronsu ne?

  15. Sai Bafarisiyen ya tashi tsaye, ya yi addu’a game da kansa yana cewa, ‘Allah, na gode maka, saboda ni ba kamar sauran mutane ba ne, wato, mafasa, masu aikata mugunta, masu zina, ko kuma kamar mai karɓar harajin nan.

  16. “Amma mai karɓar harajin ya tsaya daga nesa. Bai ma iya ɗaga kansa sama ba, sai ya buga ƙirjinsa, yana cewa, ‘Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi ne.’

  17. Amma Yesu ya kira yaran a wurinsa ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina. Kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne.

  18. Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ba zai karɓi mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga mulkin ba.”

  19. Yesu ya kalle shi ya ce, “Yana da wuya fa, masu arziki su shiga mulkin Allah!

  20. Tabbatacce, zai fi sauƙi raƙumi ya shiga ta kafar allura, da mai arziki ya shiga mulkin Allah.”

  21. Yesu ya amsa ya ce, “Abin da ba ya yiwuwa ga mutane, mai yiwuwa ne ga Allah.”

  22. Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, ba wanda ya bar gida, ko mata, ko ’yan’uwa maza, ko iyaye, ko yara, saboda mulkin Allah,

  23. Nan da nan, ya sami ganin garinsa, kuma ya bi Yesu, yana yabon Allah. Da dukan mutane suka ga wannan, sai su ma suka yabi Allah.

  24. Yayinda suna cikin sauraron wannan, sai ya ci gaba da gaya musu wani misali, domin ya yi kusa da Urushalima, kuma mutanen suna tsammani mulkin Allah zai bayyana, nan da nan.

  25. Da ya yi kusa da wurin da hanyar ta gangara zuwa Dutsen Zaitun, sai dukan taron almajirai suka fara yabon Allah, da muryoyi masu ƙarfi, da murna, saboda dukan ayyukan banmamaki da suka gani. Suna cewa,