Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. “ ‘Game da ku, tumakina, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan hukunta tsakanin tunkiya da tunkiya, da tsakanin raguna da awaki.

  2. Dole ne tumakina su ci abin da kuka tattake su kuma sha abin da kuka gurɓata da ƙafafunku?

  3. “ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce musu, duba, ni kaina zan hukunta tsakanin turkakkun tumaki da ramammun tumaki.

  4. zan cece tumakina ba za su ƙara zama ganima ba. Zan hukunta tsakanin tunkiya da tunkiya.

  5. Zan sa musu makiyaya guda, bawana Dawuda, zai kuwa lura da su; zai kula da su ya kuma zama makiyayinsu.

  6. Ni Ubangiji zan zama Allahnsu, bawana kuma Dawuda zai zama yerima a cikinsu. Ni Ubangiji na faɗa.

  7. “ ‘Zan yi alkawarin salama da su in kuma kawar wa ƙasar da namun jeji domin su zauna a hamada su kuma kwana a kurmi lafiya lau.

  8. Zan albarkace su in kuma sa tuduna kewaye da su. Zan zubo yayyafi a lokacinsa; za a kasance da yayyafin albarka.

  9. Itatuwan gona za su ba da ’ya’yansu, ƙasa kuma za tă ba da amfaninta; mutane za su zauna lafiya a ƙasarsu. Za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na karya karkiyarsu, na cece su daga hannun waɗanda suka bautar da su.

  10. Zan tanada musu ƙasar da aka sani don hatsinta, ba za su kuma ƙara zama abin da yunwa za tă fara musu a ƙasa ba ko su sha zargin sauran al’ummai.

  11. Sa’an nan za su san cewa ni, Ubangiji Allahnsu, ina tare da su kuma cewa su, gidan Isra’ila, mutanena ne, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  12. Ku tumakina, tumakin wurin kiwona, mutanena ne, ni kuwa Allahnku ne, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”

  13. Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

  14. ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kai, Dutsen Seyir, zan kuma miƙa hannuna gāba da kai in mai da kai kango.

  15. Zan mai da garuruwanka kufai za ka kuma zama kango. Sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.

  16. saboda haka muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, zan sa a zub da jininka zan kuwa fafare ka. Da yake ba ka ƙi zub da jini ba, zub da jini zai fafare ka.

  17. Zan mai da Dutsen Seyir kango in kuma yanke dukan waɗanda suke shiga da fita a cikinka.

  18. Zan cika duwatsunka da matattu; waɗanda aka kashe da takobi za su fāɗi a kan tuddanka, da cikin kwarurukanka, da cikin dukan kwazazzabanka.

  19. Zan mai da kai kango har abada; ba za a zauna a cikin garuruwanka ba. Sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.

  20. “ ‘Domin kun ce, “Waɗannan al’ummai biyu da ƙasashe za su zama namu za mu kuma mallake su,” ko da yake Ni Ubangiji ina a can,

  21. saboda haka muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, zan sāka maka gwargwadon fushi da kuma kishin da ka nuna a ƙiyayyarsu da ka yi zan kuma sanar da kaina a cikinsu sa’ad da na hukunta ka.

  22. Sa’an nan za ka san cewa Ni Ubangiji na ji duk abubuwan banzan da ka faɗa a kan duwatsun Isra’ila. Ka ce, “An mai da su kango an kuma ba mu su mu cinye.”

  23. Ka yi fariya a kaina, ka kuma yi magana a kaina ba gaggautawa, na ji shi sarai.

  24. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa yayinda dukan duniya take farin ciki, zan mai da kai kango.

  25. Domin ka yi farin ciki sa’ad da gādon gidan Isra’ila ya zama kufai, haka zan yi da kai, ya Dutsen Seyir, kai da dukan Edom. Sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.’ ”