Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. “ ‘Da wa cikin itatuwan Eden za a kwatanta da kai cikin girma da daraja? Duk da haka kai ma, za a yi ƙasa da kai tare da itatuwan Eden zuwa ƙarƙashin ƙasa; za ka kwanta a cikin marasa kaciya, tare da waɗanda aka kashe da takobi. “ ‘Fir’auna ke nan da dukan jama’arsa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”

  2. A shekara ta goma sha biyu, a wata na goma sha biyu a rana ta fari, maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

  3. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Da taron jama’a masu yawa zan jefa abin kamun kifi a kanka, za su kuwa jawo ka da abin kamun kifi.

  4. Zan jefar da kai a ƙasa zan jefa ka a fili. Zan sa dukan tsuntsayen sararin sama su zauna a kanka dukan namun jeji na duniya kuma za su ƙosar da kansu a kanka.

  5. Zan baza namanka a kan duwatsu in kuma cika kwaruruka da gawarka.

  6. Zan jiƙa ƙasar da jininka mai gudu har zuwa duwatsu, magudanan ruwa za su cika da namanka.

  7. Sa’ad da na shafe ka, zan rufe sammai in duhunta taurarinsu; zan rufe rana da girgije, wata kuwa ba zai ba da haskensa ba.

  8. Dukan haskokin sammai za su zama duhu a kanka; zan kawo duhu a kan ƙasarka, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  9. Zan dami zukatan mutane masu yawa sa’ad da na kawo maka hallaka a cikin al’ummai, a cikin ƙasashen da ba ka taɓa sani ba.

  10. Zan sa mutane da yawa su giggice saboda abin da ya same ka, sarakunansu kuma za su yi rawar jiki saboda kai sa’ad da na kaɗa takobina a gabansu. A ranar fāɗuwarka kowannensu zai yi rawar jiki a kowane lokaci saboda ransa.

  11. “ ‘Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Takobin sarkin Babilon zai auko maka.

  12. Zan sa jama’arka su mutu ta wurin takuban ƙarfafan mutane, masu bantsoro na dukan al’ummai. Za su lalatar da girman kan Masar, su kuma tumɓuke dukan jama’arta.

  13. Zan hallaka dukan dabbobinta da suke kusa da ruwaye masu yawa ƙafar mutum ba zai ƙara damunsa ko kofaton dabba ya gurɓata shi.

  14. Sa’an nan zan sa ruwanta su kwanta in sa rafuffukanta su gudu kamar mai, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  15. Sa’ad da na mai da Masar kufai na kuma raba ƙasar da abin da take cike da shi, sa’ad da na bugi dukan waɗanda suke cikinta, a sa’an nan ne za su san cewa ni ne Ubangiji.’

  16. “Wannan ne makokin da za a yi mata. ’Yan matan al’ummai za su rera shi; gama Masar da dukan jama’arta za su rera shi, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”

  17. A shekara ta goma sha biyu, a rana ta goma sha biyar ga wata, maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

  18. “Fir’auna, shi da dukan sojojinsa, za su gan su zai kuma ta’azantu domin dukan jama’arsa da aka kashe da takobi, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  19. Ko da yake na sa ta haddasa tsoro a ƙasar masu rai, Fir’auna da dukan jama’arsa za su kwanta a cikin marasa kaciya, tare da waɗanda aka kashe da takobi, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”

  20. Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

  21. “Ɗan mutum, yi magana da mutanen ƙasarka ka faɗa musu cewa, ‘Sa’ad da na kawo takobi a kan ƙasar, mutanen ƙasar kuwa suka zaɓi ɗaya daga cikin mutanensu suka mai da shi mai tsaro,

  22. Amma a ce mai tsaron ya ga takobi yana zuwa bai kuwa busa ƙaho don yă faɗakar da mutane ba sai takobi ya zo ya ɗauki ran waninsu, za a kawar da wannan mutum saboda zunubinsa, amma zan nemi hakkin jinin mutumin a kan mai tsaron.’

  23. “Ɗan mutum, na mai da kai mai tsaro bisa gidan Isra’ila; saboda haka ka ji abin da zan faɗa ka kuma gargaɗe su.

  24. Sa’ad da na ce wa mugu, ‘Ya mugun mutum, tabbatacce za ka mutu,’ kai kuma ba ka yi magana don ka juyar da shi daga hanyoyinsa ba, wannan mugun mutum zai mutu domin zunubinsa, zan kuma nemi hakkin jininsa a kanka.

  25. Ka faɗa musu, ‘Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ba na jin daɗin mutuwar mugu, amma a maimako haka ya fi su juye daga hanyoyinsu su rayu. Ku juye! Ku juye daga mugayen hanyoyinku! Don me za ku mutu, ya gidan Isra’ila?’