Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. A cikinki mutane suna karɓan cin hanci don su yi kisankai; kina ba da rance da ruwa da ƙari, kina kuma cin riba a kan maƙwabcinki ta wurin ƙwace. Kina kuma manta da ni, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  2. “ ‘Tabbatacce zan tafa hannuwana a kan ƙazamar riba da kika ci da jinin da kin zubar a cikinki.

  3. Ƙarfin halinki zai jure ko kuwa hannuwanki za su yi ƙarfi a ranar da na gamu da ke? Ni Ubangiji na faɗa, zan kuma aikata.

  4. Zan watsar da ke cikin al’ummai in warwatsa ke cikin ƙasashe; zan kuma kawo ƙarshen rashin tsarkinki.

  5. Sa’ad da ki ƙazantu a idanun al’umma, za ki san cewa ni ne Ubangiji.’ ”

  6. Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

  7. “Ɗan mutum, gidan Isra’ila ta zama ƙwan maƙera a gare ni; dukansu tagulla ne, kuza, ƙarfe da darma da suka rage a tanderu. Su ƙwan maƙerar azurfa ne kawai.

  8. Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin ku duka kun zama ƙwan maƙera, zan tattara ku a Urushalima.

  9. Kamar yadda mutane sukan tattara azurfa, tagulla, ƙarfe, darma da kuza a cikin tanderu don su narkar da su da wuta, haka zan tattara ku cikin fushina da kuma hasalata in sa ku cikin birnin in narkar da ku.

  10. Zan tattara ku zan kuma hura muku wutar hasalata, za ku kuma narke a cikinta.

  11. Kamar yadda azurfa kan narke a tanderu, haka za ku narke a cikinta, kuma za ku san cewa Ni Ubangiji na zubo muku da zafin fushina.’ ”

  12. Har yanzu maganar Ubangiji ta zo gare ni cewa,

  13. Firistocinki suna karya dokokina, sun ƙazantar da tsarkakan abubuwana; ba sa bambanta tsakanin tsarki da marar tsarki; suna koyarwa cewa babu bambanci tsakanin marar tsarki da mai tsarki; suna kuma rufe idanunsu ga kiyaye Asabbataina, da haka suke saɓon sunana.

  14. Annabawanki sun yi wa waɗannan ayyuka shafe da farar ƙasa ta wurin wahayin ƙarya da duban ƙarya. Suna cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa’ alhali kuwa Ubangiji bai faɗa ba.

  15. “Na nemi mutum guda a cikinsu wanda zai gina katanga ya tsaya a gabana a tsakani a madadin ƙasar don kada in hallaka ta, amma ban sami ko ɗaya ba.

  16. Saboda haka zan zuba hasalata a kansu in cinye su da wutar fushina, ina ɗora alhakin ayyukansu a bisa kawunansu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”

  17. Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

  18. Sunan babbar Ohola, ƙanuwarta kuwa Oholiba. Sun zama nawa suka kuma haifi ’ya’ya maza da mata. Ohola ita ce Samariya, Oholiba kuwa ita ce Urushalima.

  19. “Ohola ta shiga karuwanci yayinda take zamana; ta kuwa yi ta kai da kawowa da kwartayenta, Assuriyawa, mayaƙa

  20. “Saboda haka na bashe ta ga kwartayenta, Assuriyawa, waɗanda ta yi ta kai da kawowa a cikinsu.

  21. Na ga cewa ita ma ta ƙazantar da kanta; dukansu biyu sun bi hanya guda.

  22. Sa’ad da ta ci gaba da yin karuwancinta a fili ta kuma nuna tsiraicinta, sai na ji ƙyamarta, na rabu da ita, kamar dai yadda na rabu da ’yar’uwarta.

  23. “Saboda haka, Oholiba, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan zuga kwartayenki su yi gāba da ke, su waɗanda kika ji ƙyamarsu, zan kuma kawo su su yi gāba da ke daga kowane gefe,

  24. Za su yi gāba da ke da kayan yaƙi, kekunan yaƙi da kekunan doki da mutane masu yawa; za su ja dāgā a kanki a kowane gefe da garkuwoyi manya da ƙanana da kuma hulunan kwano. Zan miƙa ke gare su don hukunci, za su kuma hukunta ki bisa ga shari’arsu.

  25. Zan nuna fushin kishina a kanki, za su kuwa wulaƙanta ki da fushi. Za su yanke hancinki da kunnuwanki, waɗanda suka rage miki kuma za a kashe su da takobi. Za su kama ’ya’yanki maza da mata, waɗanda suka rage miki kuwa za a ƙone su da wuta.