- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
God
Ayoyin da suka ambaci God
Ka tuna da bayinka Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, waɗanda ka rantse da kanka cewa, ‘Zan mai da zuriyarka kamar taurarin sama kuma zan ba wa zuriyarka wannan ƙasa wadda na yi musu alkawari, za tă kuma zama abin gādonsu har abada.’ ”
Sai Ubangiji ya yi juyayi, bai kuwa kawo wa mutanensa bala’in da ya yi niyya ba.
Allunan aikin Allah ne; rubutun kuma rubutun Allah ne, da ya zāna a kan alluna.
Musa ya amsa ya ce, “Ba ƙarar nasara ba ce, ba ƙarar wanda yaƙi ya ci ba ne; ƙarar waƙa ce nake ji.”
Saboda haka sai ya tsaya a ƙofar sansani ya ce, “Duk wanda yake na Ubangiji yă zo wurina.” Sai dukan Lawiyawa suka taru wurinsa.
Sa’an nan ya ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Kowane mutum yă rataya takobinsa, yă kai yă kawo daga wannan gefe zuwa wancan cikin sansani, kowa yă kashe ɗan’uwansa, da abokinsa, da kuma maƙwabcinsa.’ ”
Sa’an nan Musa ya ce, “An keɓe ku ga Ubangiji a yau, gama kun yi gāba da ’ya’yanku da ’yan’uwanku, ya kuma albarkace ku a wannan rana.”
Kashegari Musa ya ce wa mutane, “Kun yi zunubi mai girma. Amma yanzu zan hau wurin Ubangiji; wataƙila zan iya yin kafara domin zunubinku.”
Don haka Musa ya koma wurin Ubangiji ya ce, “Kaito, mutanen nan sun yi zunubi mai girma! Sun yi wa kansu allolin zinariya.
Amma yanzu, ina roƙonka ka gafarta zunubinsu, in ba haka ba, to, ka shafe ni daga littafin da ka rubuta.”
Ubangiji ya amsa wa Musa, “Duk wanda ya yi mini zunubi, shi zan shafe daga littafina.
Yanzu tafi, ka jagoranci mutanen zuwa inda na yi zance, mala’ikana kuma zai sha gabanku. Duk da haka sa’ad da lokaci ya yi da zan yi horo, zan hore su domin zunubinsu.”
Ubangiji kuwa ya bugi mutanen da annoba, saboda abin da suka yi da ɗan maraƙin da Haruna ya yi.
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka bar wannan wuri, kai da mutanen da ka fito da su daga Masar, ka haura zuwa ƙasar da na alkawarta da rantsuwa wa Ibrahim, Ishaku da Yaƙub cewa, ‘Zan ba zuriyarka.’
Zan aika da mala’ika a gabanka in kuma kori Kan’aniyawa, Amoriyawa, Hittiyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa.
Ka haura zuwa ƙasar da take zub da madara da zuma. Amma ba zan tafi tare da ku ba, saboda ku mutane ne masu taurinkai domin mai yiwuwa in hallaka ku a hanya.”
Gama Ubangiji ya riga ya ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Ku mutane ne masu taurinkai. In na yi tafiya da ku ko na ɗan lokaci, mai yiwuwa in hallaka ku. Yanzu sai ku tuɓe kayan adonku, zan kuwa yanke shawara a kan abin da zan yi da ku.’ ”
Musa fa ya saba ɗaukan tenti yă kafa shi a bayan sansani da ɗan nisa, yana kiransa “Tentin Sujada.” Duk wanda yake neman wani abu daga wurin Ubangiji sai yă tafi Tentin Sujada a bayan sansani.
Yayinda Musa ya shiga cikin tentin, sai al’amudin girgije yă sauko, yă tsaya a ƙofar yayinda Ubangiji yana magana da Musa.
Ubangiji yakan yi magana da Musa fuska da fuska, kamar yadda mutum yake magana da abokinsa. Sa’an nan Musa yă koma sansani, amma saurayin nan Yoshuwa ɗan Nun mai taimakonsa ba ya barin tentin.
Musa ya ce wa Ubangiji, “Kana ta faɗa mini cewa, ‘Ka jagoranci mutane nan,’ amma ba ka faɗa mini wanda zai tafi tare da ni ba. Ga shi ka ƙara ce mini, ‘Na san ka, na san sunanka, ka kuma sami tagomashi a wurina.’
In ka ji daɗina, ka koya mini hanyarka don in san ka, in kuma ci gaba da samun tagomashi daga gare ka. Ka tuna cewa wannan al’umma mutanenka ne.”
Ubangiji ya amsa ya ce, “Zan tafi tare da kai, zan kuma rage maka nauyin kaya.”
Musa kuwa ya ce masa, “In ba za tă tafi tare da mu ba, to, kada ka ɗaga mu daga nan.
Yaya wani zai sani ko ka ji daɗina da kuma mutanenka, in ba ka tafi tare da mu ba? Mene ne kuma zai bambanta ni da mutanenka daga sauran jama’ar da suke a duniya?”