Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Raina ya tafke da marmari don cetonka, amma na sa zuciyata a maganarka.

  2. Idanuna sun gaji, suna jiran alkawarinka; Na ce, “Yaushe za ka ta’azantar da ni?”

  3. Ko da yake ni kamar salkar ruwan inabi ne a cikin hayaƙi, ban manta da ƙa’idodinka ba.

  4. Har yaushe bawanka zai yi ta jira? Yaushe za ka hukunta masu tsananta mini?

  5. Masu girman kai sun haƙa mini rami, sun ƙetare dokarka.

  6. Dukan umarnanka abin dogara ne; ka taimake ni, gama mutane suna tsananta mini ba dalili.

  7. Sun kusa gama da ni a duniya, amma ban bar bin farillanka ba.

  8. Ka kiyaye raina bisa ga ƙaunarka, zan kuwa yi biyayya da farillan bakinka.

  9. Maganarka, ya Ubangiji madawwamiya ce; tana nan daram a cikin sammai.

  10. Amincinka yana cin gaba cikin dukan zamanai; ka kafa duniya ta kuma dawwama.

  11. Dokokinka sun dawwama har yă zuwa yau, gama dukan abubuwa suna maka hidima.

  12. Da ba don dokarka ce farin cikina ba, da na hallaka a cikin azabana.

  13. Ba zan taɓa manta da farillanka ba, gama ta wurinsu ne ka kiyaye raina.

  14. Ka cece ni, gama ni naka ne; na yi ƙoƙarin neman farillanka.

  15. Mugaye suna jira su hallaka ni, amma zan yi ta tunani a kan farillanka.

  16. Ga duk cikakke na ga kāsawa; amma umarnanka ba su da iyaka.

  17. Kash, ga yadda nake ƙaunar dokarka! Ina tunani a kanta dukan yini.

  18. Umarnanka suna sa in zama mai hikima fiye da abokan gābana, gama kullum suna tare da ni.

  19. Ina da ganewa sosai fiye da dukan malamaina, gama ina tunani a kan farillanka.

  20. Ina da ganewa fiye da dattawa, gama ina biyayya da farillanka.

  21. Na kiyaye ƙafafuna daga kowace muguwar hanya domin in yi biyayya da maganarka.

  22. Ban rabu da dokokinka ba, gama kai da kanka ne ka koya mini.

  23. Ɗanɗanon maganarka akwai zaki, sun ma fi zuma zaki a bakina!

  24. Na sami ganewa daga farillanka; saboda haka ina ƙin kowace hanyar da ba daidai ba.

  25. Na yi rantsuwa na kuma tabbatar da shi, cewa zan bi dokokinka masu adalci.