Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Na zaɓi hanyar gaskiya; na sa zuciyata a kan dokokinka.

  2. Na riƙe farillanka kankan, ya Ubangiji; kada ka sa in sha kunya.

  3. Ina gudu a kan hanyar umarnanka, gama ka ’yantar da zuciyata.

  4. Ka koya mini Ya Ubangiji, don in bi ƙa’idodinka; sa’an nan zan kiyaye su har ƙarshe.

  5. Ka ba ni ganewa, zan kuwa kiyaye dokarka in kuma yi biyayya da ita da dukan zuciyata.

  6. Ka bi da ni a hanyar umarnanka, gama a can zan sami farin ciki.

  7. Ka juye zuciyata wajen farillanka ba wajen riba ta sonkai ba.

  8. Ka juye idanuna daga abubuwa marasa amfani; ka kiyaye raina bisa ga maganarka.

  9. Ka cika alkawarinka ga bawanka, saboda a ji tsoronka.

  10. Ka kawar da shan kunyar da nake tsoro, gama dokokinka nagari ne.

  11. Ina marmarin farillanka ƙwarai! Ka kiyaye raina cikin adalcinka.

  12. Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zo gare ni, ya Ubangiji, cetonka bisa ga alkawarinka;

  13. sa’an nan zan amsa wa masu cin mutuncina, gama na dogara ga maganarka.

  14. Kada ka ƙwace maganarka daga bakina, gama na sa zuciyata a dokokinka.

  15. Kullayaumi zan yi biyayya da dokokinka, har abada abadin.

  16. Zan yi ta yawo a sake gama na nemi farillanka.

  17. Zan yi maganar farillanka a gaban sarakuna ba kuwa za a kunyata ni ba,

  18. gama ina farin ciki da umarnanka saboda ina ƙaunarsu.

  19. Na ɗaga hannuwana ga umarnanka, waɗanda nake ƙauna, ina kuma tunani a kan ƙa’idodinka.

  20. Tuna da maganarka ga bawanka, gama ka ba ni bege.

  21. Ta’aziyyata cikin wahalata ita ce alkawarinka yana kiyaye raina.

  22. Masu fariya suna yi mini ba’a ba tare da an hana su ba, amma ban rabu da dokar ba.

  23. Na tuna da dokokinka na tun dā, ya Ubangiji, na kuwa sami ta’aziyya a cikinsu.

  24. Fushi ya kama ni saboda mugaye, waɗanda suka keta dokokinka.

  25. Da dare na tuna da sunanka, ya Ubangiji, zan kuwa kiyaye dokarka.